Hanyoyin adana Harshe

Hanyoyin adana Harshe

 

HANYOYIN ADANA HARSHE

           Gabatarwa

 

      Hausa na daga cikin harsuna iyalan Chadic daga tushen Afro-Asiatic, kuma harshe mafi yaduwa da  amfani da shi a cikin  Saharar Afirka. Mutane da yawa suna amfani da shi a matsayin harshen uwa, a yayin da wasu kuma suke amfani da shi a matsayin harshen hulda  (Ikara: 1991, Abraham 1962 da Robinson: 1925). Hausawa su ne majiya harshen Hausa, da ke zaune a Nijar da arewacin Nijeriya, wadan da yawan su kuma ya kai miliyan ashirin da hudu (http.//en.wikepedia: 2006 da http://www.enthnologue.com). Akwai kuma kimanin mutane miliyan sha-biyar da ba Hausawa ba ne, wadanda kuma ke zaune tare da al’umma da ke kunshe ko kuma makwabtaka da mazaunin Hausawa.            

Baya ga masu amfani da harshen a matsayin harshen uwa, akwai kuma masu amfani da shi a matsayin harshen hulda a Afirka ta Yamma (Accra da Abidjan da Dakar da Lome da Cotonou da Conakry da Banjul da Ouagadougou da Freetown da Monrovia da sauransu), Afirka ta Tsakiya (Doula da Yaounde da Maroua da Garoua da Ndjamena da Bangui da Libreville da sauransu) da kuma Wurno a kasar Sudan.

 

     Hausa ta kunshi karuruwan harshe da akan karkasa su a matsayin karuruwan yamma da gabas da kudu da kuma na arewa. Wadannan karuruwa sun hada da Kananci da Dauranci da Katsinanci da Sakkwatanci da Zazzaganci da Bausanci da Arewanci da Hadejanci da Guddiranci. Karin Kano shi ne ake dauka a matsayin mafi kusanci da ‘daidaitaccen kari’. Akwai kuma wasu ‘yan bambance-bambance kamar karin harshen mutanen Ghana da ke kama da na Sierraleone da ke da kamanci ta fuskar nahawu da karin Sakkwatanci (Wikepedia: 2006). Akwai kuma wasu ‘yan bambance-bambance da ake samu daga wadanda ba majiya harshen ba ne. Harshen Hausa yana da matsayin harshen hukuma a arewacin Nijeriya, in da ake amfani da shi a mahawarori da sauran ayyukan majalisu. Haka kuma yana da matsayin harshen kasa a Nijar, inda ake gudanar da nazarce-nazarce na ilimi da adanawa. Wadannan ayyuka suna samun kulawa ta musamman a jami’o’i da cibiyoyin bincike da kuma wasu hukumomi a Britain da America da Germany da Poland da Japan da China da Libya da Ghana da sauransu. A Nijeriya da Nijar kuwa, ana gudanar nazarce-nazarce da bincike-binciken Hausa a jami’o’i da sashe-sashe na kimiyar harshe da kuma cibiyoyin harsunan Afirka. Ana nazarin Hausa a manyan makarantu da kwalejojin ilimi a Nijeriya, ana kuma koyar da Hausa a makarantun firamare da sakandare. Hasali ma, tana daya daga cikin manyan harsunan da kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (CFRN, 1999) ya yi wa tanadi na amfani da shi a majalisar tarayya. Kafafen yada labarai na duniya daban-daban ma suna amfani da Hausa, kamar BBC da Voice of America da Deutche velle da Radio France International da Voice of Russia da China Radio International (Beijing) da kuma Iran Radio. Haka kuma ana amfani da Hausa domin sadarwa ta kafafen rediyo da talabijin a Nijar da Nijeriya. Bugu da kari, ana amfani da Hausa a matsayin kafa ta rubuta littattafai da jaridu da kuma sauran ayyukan adabi. Da harshen ne kuma ake tafiyar da harkokin finafinai da bidiyo a yammacin Afirka.

 

Bayanin da ya gabata kumshiya ce cikin tasirin Hausa a Afirka ta yamma da Afirka da kuma duniya gaba daya. Idan aka yi tsokaci za a samu nau’o’i na ilimi mabambanta kuma masu ban sha’awa, wato kwatankwacin tarihi da addini da kimiyar harshe da kamus-kamus da adabi da kuma aikin jarida. Alkiblarmu dai a wannan makala ita ce tsokaci dangane da tsare-tsaren gargajiya da samuwar rubutu da kuma hanyoyin sadarwa na zamani ga al’ummar Hausawa.

Daga nan kuma sai bayani dangane da tarihin rubutu da kuma hanyoyin sadarwa na zamani da kuma barazanarsu ga adana harshen Hausa da kuma al’adun Hausawa.

  Za mu  ci gaba 

Daga Alkalamin Farfesa Salisu Ahmad Yakasai