Mahaifin Sanata Ndume; Alhaji Buba Ali ya rasu

Mahaifin Sanata Ndume; Alhaji Buba Ali ya rasu

Daga Muhammad Shamsudeen, Borno.

Da safiyar yau, Sanata mai wakiltar shiyyar Kudancin Borno a zauren majalisar dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume ya sanar da rasuwar mahaifin shi, Alhaji Ali Buba Ndume.

Sanatan ya bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, wadda aka rabawa manema labaru yau (Talata) a Abuja. Tare da bayyana cewa yau za a yi jana'izarsa a birnin Maidugurin jihar Borno. 

Sanarwar ta bayyana cewa, “A cikin halin alhini nake sanar da rasuwar Alhaji Ali Buba Ndume, mahaifin Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ya rasu safiyar yau a birnin Maiduguri." 

“Ubangiji Allah ya yafe masa kurakuransa tare da bai wa iyalai hakurin jure wannan babban rashin."

Bugu da kari kuma, sanarwar ta bayyana cewa, “Haka kuma za a gudanar da sallar jana'izar marigayi Alhaji Ali Buba Ndume, da misalin karfe 4:00 na yamma a kofar gidan Sanata Mohammed Ali Ndume dake kan titin Damboa kusa da ofishin NTA a birnin Maiduguri.”