Wamakko ya roki gafarar Allah ga  mutane 22 da gishirin lalle ya kashe a Sakkwato

Wamakko ya roki gafarar Allah ga  mutane 22 da gishirin lalle ya kashe a Sakkwato

Daga Muhammad M. Nasir.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya roki gafarar Allah ga mutane 22 da gishirin lalle ya yi sandiyar barinsu duniya a kauyen Danzange cikin karamar hukumar Isa a jihar Sakkwato.

Sanata Wamakko ya yi addu’ar ne a lokacin da yake  addu’a ta musamman ga margayan   amadadin magoya bayansa da dukkan masu yi wa jihar Sakkwato fatan alheri.

Honarabul Malami Muhammad Galadanchi a zantawarsa da Managarciya ya ce Sanata Wamakko ya shirya addu’ar ne a matsayin ta’aziya ga iyalan margayan domin abu ne da Allah ya kawo kuma a wurinsa ne za a nemi gafara, da rokon ya karbi shahadar mutanen ya baiwa dangi da al’ummar Sakkwato hankurin rashin margayan.

Sanata Wamakko wanda yake tsohon gwamnan Sakkwato ne bayan mika sakon ta’aziyarsa ya roki Allah ya kawowa jihar Sakkwato da Nijeriya zaman lafiya kan rashin tsaron da take fama da shi.

A ranar Assabar data gabata mutanen kauyen Danzange  suka hadu da waki'ar rasa mutum 22 a lokaci guda bayan sun ci abinci mai guba.

Margayiyar matar Hamidu Makeri ce ta yi abincin da ta zuba gishirin lalle a cikin kuskure suka ci tare da ‘ya’yanta hudu da matan aure biyar da sauran kananan yaran gida, kwana daya bayan cin abinci suka kamu da ciwon ajali, an kai su asibiti kan amai da suka rika  yi, sun samu sauki aka sallame su bayan dawowarsu gida ne suka bar duniya.