Cibiyar TIC Ta Horar Da Matasa Sama Da Dubu Daya Kan Sana'o'in Hannu Da Kere-kere A Neja

Cibiyar TIC Ta Horar Da Matasa Sama Da Dubu Daya Kan Sana'o'in Hannu Da Kere-kere A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.

Cibiyar horar da sana'o'in hannu da kere-kere ( Technology Incubation Centre) ta horar da mata da matasa dubu a wannan shekarar kan kananan sana'o'in hannu mabanbanta. Shugaban cibiyar, Injiniya Umar Alhaji ne ya bayyana hakan a taron wuni daya na masu kananan masana'antu da matsakaita dan samun hadin kan yadda kasar nan za ta dogara da kafarta.

Alhaji Umar, ya cigaba cewar tana da sassa da dama na koyon sana'ar hannu da kere-kere wanda bayan horarwa cibiyar na hada masu kananan masana'antu marasa karfi da manyan masana'antu ta yadda kayayyakin da ake samarwa zasu yi tasiri a kasuwa.
Wannan shekarar mun horar da matasa da mata sama da dubu daya kuma muna da hadin guiwa da hukumomin gwamnati masu sanya idanu a ingancin kayayyakin da ake samarwa a kasa dan kaucewa yaduwar kayayyakin da ba su da inganci da zasu iya zama barazana ga lafiyar bil'adam. Yau muna da shekaru ashirin da gwamnati ta kafa hukumar nan kuma a koda yaushe muna aiki ba dare ba rana dan ganin mun cigaba horarawa da koyar da sana'o'in hannu ga yan kasa.
Da yake bayani ga mahalarta taron, babban daraktan hukumar kula da kananan sana'o'i ta jiha, Malam Ahmad Shu'aibu Gwada, yace gwamnatin jiha tayi tanadin wasu kudade dan bada tallafi ga masu kananan sana'o'in musamman saboda yadda annobar Korona tai silar durkushewar wasu kananan yan kasuwa. A cewarsa shirin na bankin duniya ne, gwamnatin jiha bisa jagorancin Alhaji Abubakar Sani Bello ta ga dacewar bada ta ta gudunmawar ta hanyar kebe wasu kudaden daga aljihunta dan tallafawa ga kananan yan kasuwa.
Yace hukumar SME, tana da shirye shirye da dama da take muradin gabatarwa a jihar dan tallafawa manya da kananan yan kasuwa, amma wajibi sai an bi ka'idodin da hukumar ta tsara, akwai shirin rance sannan akwai wanda kyauta ne saboda karfafa guiwar masu kananan masana'antu da kasuwanci ta yadda zasu iya samun tsayawa da kafafuwan su wanda zai taimakawa gwamnati wajen rage yawan rashin aikin yi a cikin jama'ar jihar.
Ahmad Gwada, ya sha alwashin bisa jagorancinsa zai samar da kididdigar kananan yan kasuwa da matsugunnansu ta yadda duk wani tallafin da zai zo zasu samu damar cin moriyarsa, ya bayyana cewar a kowani lokaci kofarsu a bude take ga manya da matsaikatan kamfanoni dan ba su shawarwari da tallafin yadda kasuwancin su zai cigaba.
Alhaji Haruna Usman (Dan Majen Wasse) shi shugaban tsare-tsare da hadin guiwa tsakanin hukumar TIC da gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci, ya bayyana wa shafin jaridar Managarciya cewar, shirye shiryen da yan siyasa ke gabatarwa na horar da matasa da zasu yi hadin guiwa da cibiyarsu da zai fi tasiri, domin bayan horarwa suna da dubarun sanya idanu da hada karamin dan kasuwa da manyan kasuwanni ta yadda abinda ya koya zai yi tasiri a kasuwa.
Dan Maje, ya cigaba da cewar mafi yawan lokutta, matasan da yan siyasar ke horarwa ba su da sha'awa akan abinda aka horar da su illa yunkurin karban dan karshen shirin su tsira da tallafin da zasu samu wanda a karshe su kadar da shi. Amma my TIC muna da dubarun kulawa da bada shawarwarin irin sana'ar da ya dace mutum ya koya da kuma sanya idanu a dan kankanin lokaci mu tabbatar mun koyar da shi da kuma taimaka masa wajen ganin ya shiga kasuwa.
Bankuna da dama, da hukumar NAFDAC, SON, SME, SMEDIN na daga cikin wadanda suka halarci taron kuma sun yiwa kananan yan kasuwan da manya bayanin yadda zasu iya cin ribar hukumomin su ba tare da sun fada hannun baragurbi ba.