GOSHI: Fita Ta Huɗu

GOSHI: Fita Ta Huɗu

GOSHI

_*MALLAKAR*_
_*Umma Yakubu Imam(Maman Dr)*_


P-4


Adda Hauwa, Baffa, Goshi suka shigo gidan kai tsaye, in da Goshi ta nufi ma'adanar ajiye kujerar zama ƴar tsugune tare da saurin ɗaukowa ta direwa Adda Hauwa ta hau kai ta zauna cikin kuka da shassheƙa tana mai cigaba da cewa, "Tsakaninka da Allah Ibrahimu na taɓa cewa matarka Amina ba ni ƙaunar ƴaƴa mata sai maza Ibrahimu kar ka ɓoye min me na taɓa musgunawa Amina acikin gidanka kafin na dawo nan da zama? Ko na taɓa yunƙurin nunawa Amina tsana ko kyara, baƙar magana a zaman da muka yi da ita? Hankalin baffa idan ya yi dubu ya tashe ya ce, "Ko ɗaya Adda halin Amina na rashin mutunci kaɗan kika gani
daga cikin ɗari sam batada kunya amma in sha Allahu daga wannan karon ba za ta kuma ba in dai sunana Ibrahim kuma ɗa a gareki Adda ina haɗaki da girman Allah ki yi haƙuri kuma aure na shirya da izinin Allah rana ita yau da aurena akan Uwani. Duk da kukan da Adda Hauwa ke yi bai hanata ɗago kai a razane ta dubi baffa da yake dubanta cikin sauri Adda Hauwa ta ce, "A hir ɗinka baffa kar in ji kuma kar in gani ka rabu da Amina domin akwai zuri'a atsakaninku ko ba komai mun riga da mun zama ɗaya. Batu na amsa auren Uwani kuma da ka yi ya wanken zuciyata fes, fatana Allah ya sa abokiyar arziƙinka ce ya kauda abin ƙi.

"Amin Addata, shi ke nan ni ma baffa zai yi mani anti ni da Na'ima. Cewar Goshi da ke ɓaɓɓaka dariya har da rawa, don har dariya ta baiwa Adda Hauwa da ta kai mata ranƙwashi aka kafin baffa ya korata ɗaki ya cigaba da baiwa Adda haƙuri tana kwarara masa albarka har ya yi mata sallama ya fita. 
Adda Hauwa da Goshi na zaune akan tabarma sun gama cin tuwon dawa da miyar kuɓewa ɗanya na dare Awilo ya faɗo gidan yana disko tamkar ƙafafuwansa za su karye don lanƙwasa. Karaf idanuwansa suka dira akan Goshi diskon da ya tsaya da yi ke nan ya kuma wangale baki da ƙarfi ya saki ihu tare da yowa kan Goshi a guje da tuni ta rigashi barin wajen tsabar zafin nama irin nata yana me cewa, " A'uzubikalimatullahi tammata min sharri ma kalaƙ. Adda, adda ma za ki miƙo mini dutsunan can na jefe sheɗaniyar yarinyar nan kar ta tado miki da fatalwar mijinki ta saka shi yo miki ƙwarƙwarori dubu na fatalhun mata.
Zagaye-zagaye Awilo da Goshi suka fara yi ala dole sai Awilo ya jefe Goshi da dutsuna ya kuma kamata ya tasa ƙeyarta har gidan Baffa. Lamarin da mamaki ya lulluɓe Adda Hauwa ta kasa furta komai sai kallonsu da ta ke yi baki a wangale. Ganin babu ranar dena zagayen ya sa Adda Hauwa ta shi tsulum ta shiga tsakiya Awilo sai haki yake yana cewa, "Kwarankwatsa dubu Adda sai yarinyar nan ta bar cikin gidan nan, wallahi Allah ba za ta haɗa mana masifu tukuba-tukuba da bala'i a  gida ba hegiya me zubin aljanu. "Ni ba hegiya ba ce kuma aljannu in sha Allahu yau sai sun zo maka da daddare. Cewar Gashi, ai kamar Goshi ta sake tunzura Awilo ya zaburo zai yo kan ta duk da cewar Adda na tsakiyarsu, har sai da Adda ta dake shi da hannu ta ce, "Wai kai Hamza bululluka nawa ka zuba mini a cikin gidan nan da har kake ɗaɗɗaga jijiyar wuya sai jikata ta bar gidan? 

"Idan ita jikar ki ce ni kuma tsintoni kika yi a juji ko sadaka aka baki ni Adda? Na fa gaji da nuna mini wariyar launin fatar da kike yi a gidan nan don an ga uwata ta mutu shi ne ake musguna mini ake tsangwamata, me ya sa kika tafi kika bar ni Innata ki zo kawai ki ɗauke ni mu tafi barzahu tare tun da baba ya sallamawa muguwar tsohuwar nan ta cigaba da jiran duniyar kowa ma ya huta. Kuma wallahi tun da na ce yarinyar nan sai ta fita daga gidan nan duk dare ta koma gidansu ba za ta kwana a gidan nan ba, uwarta fa ta yo wa kishiya ke kuma kika san me za ta jajiɓo miki a nan gaba? Ran Adda Hauwa a ɓace ta amsawa Awilo da cewa, "Idan ka gama zagin nawa abin da ya saura maka kawai ka kawon duka ka ji daɗi, kuma uban naka zai zo ya sameni sai ka maimaita abin da ka ce mara ɗa'a da mutunci idan ka isa ka zo ka taɓa Goshi ka ga abin da zan yi maka. Ƙafa Awilo ya ɗaga guda ɗaya ya daki ƙasa kafin ya yi ɗakinsa fuuu ya shiga tare da banko ƙofa Adda Hauwa ta kamo hannun Gashi suka koma kan tabarma suka zauna. Faɗa sosai Adda Hauwa ta shiga yi wa Goshi akan rashin kunyar da ta yi wa Awilo ko da da kwana ɗaya ya girmeta ya girmeta bare tsiransu shekara uku ne cif kuma ma dai ita da shi duk ɗaya tun da ɗan wa da ɗan ƙanni suke. A nan ne ma Goshi ta ce za ta koma gida kawai saboda kayan makarantarta na gobe in ya so daga can ta wuto nan tun da baffa na gida yanzu. Awilo ko na ji ya fito tsakar ƙofar ɗakinsa ya tsaya yana surutai akan Goshi, wanda da ƙyar dai Adda Hauwa ta barta ta tafi gida bayan ta gargaɗeta kar ta kuskura ta tankawa kowa idan ta je har Na'ima gudun matsala. Gashi ta amsa da, 

"To!

Ta nufo ƙofa ko kallon Awilo ba ta yi ba yana harare-harare da hura ƙofofin hancinsa. A ƙofar gida Goshi ta iske baffa da ya ganta ya soma tambayarta me ya dawo da ita a daren nan? 
"Daman na manta kayan makaranta na ne baffa ka san dukan fashi ake yi shi ne na dawo ɗauka. Cewar Goshi, baffa ya tasa Goshi a gaba har cikin gida zuwa ɗakinsu ita da Na'ima da tun da ta ga shigowar Goshi take ƙwafa sai hararar Goshi take ba ta kula ta ba ta je ta ɗauko kayan makarantarta da jakarta.

Dare mahutar bawa, kasancewar lokacin sanyi ne Adda Hauwa ta shige ɗaki ta banko ƙofa har da sakata bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita tana munsharin gajiya liƙis! 
Awilon ma haka, domin kowacce gaɓa ta jikinsa ta yi tuɓus saboda rawa da lanƙwashe-lanƙwashe da ya sha yau a wajen gayu, sai dai shi bai saka sakatar ɗaki ba kasancewar ƙofarsa a karye take amma ya shige can cikin ƙurya ya lulluɓa sai goron munshari yake ja tamkar rago ga duhun da ko tafin hannuwanka ba ka iya gani. Dirumm Awilo ya jiyo saukar abu tamkar a mafarki ya ɗan buɗe ido ya rufe sakamakon tozali da duhun da ya mamaye ƙwayar idonsa har da gyara kwanciya kunnuwansa suka jiyo masa wata dakushasshiyar murya na cewa,

"Hamza ka hanani kwanciyar kabari na...

"Girgiza-girgiza... 


"Kullum dare ka na damuna...

"Girgiza-girgiza...

Ana cewa bacci ɓarawa ne amma samma ko ƙassa Awilo ya nemeshi ya rasa a ɗan lokaci kaɗan tamkar ba farkawa ya yi yanzu ba.  Nan take Awilo ya sake duƙunƙunewa a cikin bargonsa me masifar datti gabansa na dukan tara-tara bai aune ba ya ji wani ɗumi na ketowa daga cikin jikinsa zuwa ƙasan ƙafarsa karaf aka cigaba da cewa,

"Hamza taho mu tai kabarina...

"Girgiza-girgiza...

Tuni Awilo ya wangale idonsa tare da sakin wani marayan ihu yana kwarmawa Adda Hauwa kira acikin daren garin mutsu-mutsu ya shafo cocilan ɗin da ya kunnata ke nan ya yi arbu da wani abu duk jikinsa a luluɓe da farin ƙyale. Da cocilan ɗin da shi kan sa Awilon aka rasa inda suka nufa ban da ihu da buge-buge babu abin da ake jiyowa a cikin ɗakin Awilo har Allah ya sa Adda Hauwa ta farka a firgice ta kunna fitilarta tare da miƙewa cikin sauri ta buɗe ƙofa ta yo waje.

@Real Maman Dr
(2025)