MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA FITA TA SHA TAKWAS

MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA FITA TA SHA TAKWAS
          _*MEE'AD*_
                   
             
                
           
      
 
39 ~ 40     
 
   
Tin asuba data tashi bata koma bacci ba kasancewar yau zataje gidan kakarta Hajiya Hindu sbd jin gidan tayi ya mata zafi sosai, kai tsaye kitchen ta nufa dan karban break fast dinta.
 
Karfe tara da rabi ta gama shiryawa tsaf cikin riga da siket na' atamfa, tayi kyau sosai sai kamshi take zubawa, gyale ta   yafa kafin ta fita waje.
 
Da sallama ta bude kofar falon Mommy hangota tayi kan sallaya da 'alamar ta idar da sallah.
 
Shafa 'addu'an tayi sannan ta juyo fuskarta dauke da murmushi Mee'ad kin fiye rigima, na rasa mi zakije kiyi a gidan Hajiya harna tsawon kwana uku, idan ba rigima ba mi hakan yake nufi ?"
 
Shagwabe fuska Mee'ad tayi Mommy nafiso naje gidan Hajiya na hutane sbd bajin dadin zama ni d'aya 'a gidan nan nakeyi ba!
 
Dafata Mommy tayi kinga kwantar da hankalinki bani nakar zomon ba, tashi kije Allah ya kiyaye hanya.
 
Murmushi tayi tace na gode Mommy na bye, Kofar fita ta nufa.
 
Bin bayanta da kallo tayi fuskarta dauke da murmushi Allah ya shirya min ke kawai tace.
 
Bata tarar da kowa 'a babban falon gidan ba, kofar fita daga falon ta bude ta nufi harabar gidan.
 
Sannu Baba ina kwana ya tsufa kuma ? Alhmdlh yayasu Hajiya ? 
Lfynsu klau sunce na gaisheka ma, washe baki Baba mai gadi yayi kafin yace na gode sosai.
 
"Yauwa Baba ina Malam Idi yake yana kwance, amma bari nayo kiranshi.
 
Bayan sun gama gaisawa da malam idi ta bashi keys din hannunta gashi Malam kayi hakuri ka mikani gidan Hajiya Kaka. Daria yayi ya karbi keys din yace muje kawai hajiya karama! tayi murmushi muje to.
 
Amal! ki tashi kin kusa makara faah, ta bude ido a hankali Umma ke ce yau kk tashina, lallai yau za'ai ruwa da kankara.
 
Hingonki kekam ta mata dakuwa! to mijinkine yake jiranki a falo. ta tashi da hanzari ta nufi toilet dan shiryawa.
 
Daria Umman tata tayi, su Amal masu miji Allah ya kaimu bikinki musha hidima.
 
Sai da ta gama shiryawa tsaf kafin ta sauko kasa, Kai tsaye darning ta nufa dan yin break fast.
 
Ta samu darning din a cike kamar yadda ta saba samunsa, good morning all! ta ce sannan ta zauna 'a gefen Majeed ya kake Yaya ? yad'an 'bata fuska klau nake! daga haka bai kara ce mata komai ba yaci gaba da karyawansa.
 
Bayan sun gama karyawa, ya dubeta ki tashi muje karki makara ko! to kawai ta ce sannan ta tashi daga kan kujerar bye Mom and Umma see me later.
 
Bayan sun fita Abba ya dubi Hajiya Suwaiba ya ce Suwaiba yaya 'akayi yarinyar nan ta 'baci hakane ? muna matsayin iyayenta bazata iyayi mana gaisuwan mutunci ba, da zarar anyi magana kuma sai kice wai wayewa" wayewa ne ko hauka baki daya kin shagwaba yarinya.
 
Ta marai - raice murya haba Alhaji har yanzu Amal yarinya ce faah! kwafa yayi kafin ya tashi yayi part dinsa.
 
Jiki a sanyaye Hajiya Suwaiba ta rufa masa baya sbd 'bacin rai data hango a cikin idanun Alhajin.
 
%%%%%%
 
Mee'ad basu wani dade akan hanya ba suka isa. Malam idi ya sauketa a gidan takwarar taa godiya tayi masa ta shige cikin gida.
 
Bata samu kowa 'a falon ba wannan dalilin ya sanya ta nufi dakin da take sauka idan tazo gidan, a bude ta tarar da kofar shiga dakin, kutsa kai tayi ta samu dakin a share ga wani daddadan kamshi da yake tashi lumshe ido tayi kafin ta rufe kofar, waldrop ta nufa ta ajiye jakar dake hannunta, kwanciya tayi tana tinanin abinda ya faru.
 
Tinda Majeed ya dauko Amal bai ce da ita komai ba, music ya sanya yana bin bakin mawakin.
 
" Amal ta dube shi a hasale kai malam! wai mi kk nufi danine " mi nayi maka da zaka dauko ni ka wani shareni kamar ka dauko dodo.
 
"Murmushi yayi hmm Amal kenan mi kuma kikaga nayi"?
 
"Yatsine fuska tayi batace komai ba"
 
"Au ina miki magana ma kinki ki kulani ko ? "amma kinsan dalilin yin shirun nawane ?
 
"Girgiza kai tayi "
 
"Yauna wayi gari banijin dadi jiki nane shiyasa kika ganni haka.
 
Sorry Mijina! miyasa baka fadamin baka ?
 
Shiru yayi kafin yace kiyi hakuri bazan karaba kinji.?
 
Ta ce ya wuce! muje ka saukeni basai ka tsaya jiran komai ba ka dawo gida kaji ?
 
"Eh kawai yace yaci gaba da driving dinsa.
 
Hajiya suwaiba tana shiga part din Alhaji ta hangoshi zaune bisa gado ransa 'bace" jiki a sanyaye ta karasa wajenda yake ta durkusa kasa ta daura hannayen ta bisa cinyarsa ta ce Alhaji nasan nayi maka laifi, amma kayi hakuri nayi maka 'alkawarin hakan bazai ci gaba da faruwa ba.
 
Yaja dogon ajiyar zuciya kafin yace ya wuce" sai dai inaso ki zama uwata gari mai bama y'ay'ayenta tarbiyya na gari " ki dubi yanda y'ar uwarki take iya bakin kokarinta wajen bama y'ay'anta tarbiyya 'amma ke kin kasa gane hakan.
 
Tin yarinyar nan tana karama kika shagwaba ta bakison abinda zai taba miki ita ballantana abinda zai 'bata mata rai" to bari kiji duk abinda ya samu wannan yarinyar kece sanadi " dan haka nake shawartar ki da kiji tsoron Allah ki gyara tarbiyyar y'arki ko dan samun kyakkyawar sakamako a wajen mahaliccinki.
 
Hajiya Suwaiba ta ce insha Allahu zanyi iya bakin kokarina dan naga hakan ya kasance" amma ina rokonka da kayi hakuri. magiya tayita masa har ya hakura.
 
Majeed yana 'ajiyeta juyowa yayi bayan sunyi sallama.
 
Tafiya yake akan hanya zuciyarsa cike da sake - sake " tambayar kansa yake wai miyasa Amal ta zama hakane ? gefen hanya ya sauka yayi parking ya ci gaba da tinane - tinane.
 
"Tabbas halayyan Amal sunyi matukar canjawa kwata - kwata ta daina dukkan abinda na santa dashi a rubuce, ko karya take rubutamin a wancan lokacinne ?
Amal ta daina karance - karance da nasan tanayi a da caan ta daina jin 'kira'ar data sabaji ta daina komai ma".
 
"Tinanin Mee"ad ne yazo masa murmushi yayi sannan ya ce Mee'ad kenan kawata musamman" komai nata burgeni yake musamman murmushi da yanda take bani kulawa ta musamman" miss u kawata.
 
"Kunna motar yayi yaci gabada tafiya.
 
Yana isa gida kai tsaye dakin Mee'ad ya nufa ya gama le'ke - le'kensa ba tare da yaji motsin taba" falon Mommy ya wuce da sallama ya shiga bayan sun gaisane yake tambayarta ina Mee'ad ? 
 
Murmushi tayi Mee'ad ta tafi gidan Hajiya wai zatayi one weak " zaro ido yayi yace what! Mommy kika ce one weak zatayi faah" bazan barta tayi sati guda 'acan ba bari naje na sameta, gama fadin hakan keda wuya ya tashi ya nufi kofar fita. 
 
A hanzarce ya bude kofar yana shirin fita, yana budewa yayi arba da Umma tsaye bakin kofar" a tsorace Umma ta fara kame - kame aam- dama - dama naga shiganka falon ne na biyoka sbd inaso na baka sako.
 
Kura mata ido kawai yayi ya bude baki yace...
 
 
Mai karatu biyoni kasha lbr <img data-emoji="