INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Takwas

Ita kuwa Lantai tana ganinta riƙe da littafin jarumi Nasimat mai suna DORON MAGE sai farin ciki ya baibayeta cikin zaƙuwa ta tashi ta ɓoye littafin ta ɗauko wanda take karantawa wato INA DA HUJJA ta cigaba da karantawa, tana karatun tana hawaye domin dai labarin ya tsuma mata zuciya sosai da sosai.

INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Takwas

     Page 8

Ko da Malam Muntasir yadawo ya iske gidanshi a buɗe sai abin ya ba shi mamaki, lokacin daya shiga cikin gidan ya iske yadda akai ma shi da kayan ɗakin sai kawai ranshi ya ba shi sata aka shigo akai ma shi.

Cike da damuwa ya duba inda ya aje kuɗaɗensa na mota da sauran canji, abin mamaki sai ga su a inda ya barsu suke ba'a  sauya masu waje ba.

Cikin sauri ya ɗauka ya ƙirga, cif sun cika ko biyar ba'a ɗauka ba.

Shiru yayi yana tunanin to me aka zo nema a gidan ? Ya duba komi yana nan babu abin da aka ɗauka, ya gyara komi yadda yake ya kwanta yana jinjina al'amarin yadda za a shigo gidan mutum ba'a ɗauki ko tsinke ba, bayan an gama yamutsa duk abin da ke gidan?

 

Ina littafin da Nuratu ke nacin nema ?

Abin da zuciyarsa ta ambata kenan.

 

Da hanzari ya duba inda littafin yake yaga bai ganshi ba.

 

Kenan Nuratu ce tayi ma shi wannan aikin akan littafi ?

Kai ta ina Nuratu zata iya ɓalle kwaɗon dake jikin ƙofar gidan harta ɓalle na ƙofar ɗakin ?

To a cikin wane lokaci ma duk ta aikata hakan ?

Duka minti nawa yayi a gun mai shayin ?

Tabbas yana buƙatar sanin amsoshin nan yasan kuwa gun Nuratu kawai zai same su, don haka gobe ba zai tafiyar asuba ba kamar yadda ya tsara sai ya je gidansu Nuratu domin samun amsoshin tambayoyinsa.

 

Da haka ya samu barci ya ɗauke shi, da tunani kala-kala a cikin ranshi.

 

 

Ita kuwa Lantai tana ganinta riƙe da littafin jarumi Nasimat mai suna DORON MAGE sai farin ciki ya baibayeta cikin zaƙuwa ta tashi ta ɓoye littafin ta ɗauko wanda take karantawa wato INA DA HUJJA ta cigaba da karantawa, tana karatun tana hawaye domin dai labarin ya tsuma mata zuciya sosai da sosai.

"Lallai kam Hidaya dole ki ce KINA DA HUJJA domin wannan ba ƙaramar HUJJA bace ni Lantai haka abin yake ashe ?

 

Tabbas duk wanda ya biyewa son zuwa haka ke faruwa gareshi daman.

 

Hasib baka kyauta ba domin Hidaya ai mace ce, an ce kuma kun fimu hankali to akan me ka aikata hakan ?

Kuka Lantai ke yi sosai abin gwanin ban tausayi.

 

Inna Kande tana farkowa sama-sama take jin surutu da tashin kukan Lantai, sai ta fashe da kukan itama tana cewa.

"Lantai daman nasan jidali kika ɗebo mana yau ga bamu da mai ceton mu sai Allah Lantai baki kyauta ba."

 

Inna Kande kuka take tana Lantai ta jawo masu masifa da tashin hankali yayin da Lantai ke kukan Hidaya ta matuƙar bata tausayi.

 

Idanun Inna Kande a rufe suke kada ta buɗe taga wuƙar ɗazun mai walƙiya, tasan yanzu hada gayyar yaransa yayo, shike  nan ƴan Tumakai da Awakan da take kiwatawa don idan auren Lantai ya tashi ta saida ta cika mata ɗaki da jere sun kwashe su.

Ta sake rushewa da kukan takaici ta ce, "Lantai kin min, kin ma kanki don kuɗin kayan ɗakinki suka kwashe wallahi na kai ki daga ke sai tabarma ai."

 

Sai lokacin Lantai taji abin da Inna Kanden ke cewa, duk da cikin kuka take sai da ta kwashe da dariya abinta.

 

Inna Kande sai kuma wani sabon tunanin ya shigeta, sun haukata mata jika shike nan ta bani ta lalace ita ina zata saka kanta yau ?

 

Lantai ganin abin Inna Kande kamar na zauci yasa ta isa inda take kwance ta haskata da fitilar da take karatun, ganin idanun Inna Kande rufe sai hawaye wasu na korar wasu ga magana tanayi sai Lantai ta kwashe da dariya tana ƙara kallon yadda fuskar Inna Kande ta wani faɗa yau kaɗai duk ƙasusuwa sun bayyana, tsufanta ya bayyana fili.

 

Gimtse dariyar tayi ta fara kiran sunan Inna Kanden.

 

Aikuwa sai Inna Kande ta saurara jin muryar Lantai kamar ba hauka yasa ta buɗe idonta ras ta sauke su akan Lantai.

 

Lantai ta rungume ta tana cewa, "Mugun mafarki kike Inna Kande ? Naga sai kuka kike kina surutai idanunki a kulle?

 

 

Zaune Inna Kande ta tashi ta dinga duba Lantai da jikinta ganin ba abin da ya sameta ta ce, "Sun kwashe Tumakan sun tafi ko ?

Sai yanzu Lantai ta fahimci abin da ke faruwa ta kuwa fashe da dariya ta ce, "Littafina fa ya kawo min, ai Yaya Isah na sona ba zai cutar da ƙanwarsa ba Lantai."

 

Inna Kande sai ajiyar zuciya take, tabbas idan tai sake wata rana tashin hankalin Lantai ne zai kasheta.

"Ke yanzu Lantai baki gudun asan Barbushe ya sanki a wannan ƙauyen ? Kin san dai hatta mai gari sai ya kore mu daga nan ko ?

 

Lantai ko a jikinta, ita fa har mai garin tana iya sawa Barbushe yayi ma shi rashin mutunci, ai daman ba kirki gareshi ba, duk azumi sai an kawo kyautar sukari da gero daga Maraya amma bai ba kowa gidanshi ake cinyewa, abin na bata haushi don haka wannan karon idan azumi ya zo ko dai ayi raba dai-dai da gidansu ko kuma kowa ya rasa.

 

Basu ankara ba, sai jin kiran Sallah kawai su kai ta asuba nan da nan Inna Kande ta miƙe gara ko sallar ayi garin ya waye ma ta ji sauƙin tashin hankalin da take ciki ai.

 

Lantai na gama sallah ta ɗaga hannunta sama ta fara addu'a, "Ya Allah ka yafewa Hidaya kasa lafiyarta lau, Allah naji daɗi da batai abin kunyar bayyane ba, Allah kasa mata dangana...

 

Inna Kande ta bige mata baki, cike da faɗa take ce mata, "Ke yanzu har ta wasu Hidaya kike ga gagarumar matsala kin janyo mana ? Na ɗauka ji zan kina cewa Allah ka rabani da Barbushe kasa ya manta gidanmu ya manta ni ?

 

Lantai na dafe da bakinta ta ce, "Ni fa wallahi ba zan rabu da Yaya Isah ba don shima Yayana ne ai ...

Inna Kande ta sake buge bakin "Don gidanku ta ina kuka haɗu har ya zama Yayanki hanyar jirgi ko ta mota ?

 

Lantai ta miƙe ta fice daga ɗakin ta koma tsakar gida tayi fushi .

 

Inna Kande ta shareta ta kaɗa masu kunu ta bata kuɗi ta siyo masu ƙosai da goro.

 

Da ƙyar ta amshi kuɗin aiken tana cewa, "Idan kika sake doke min baki na rantse sai na kira maki shi ba ruwana ni."

 

Sai kuma Inna Kande tayi wuƙi-wuƙi domin dai Lantai bata da kirki tana aikata abin  da tace ne kai tsaye.

 

Sai Inna Kande tayi tsit, har Lantai ta fice daga gidan bata sake mata faɗa ba.

Lantai na isa gidan sai da ƙosan tana ta cika tana batsewa ta iske layi cike danƙam duk an rigata sai kawai ta wuce kowa ta shiga miƙa kuɗin ƙosanta kawai  ita abata kawai sauri take, sai kuwa yaran da suka rigata suka fara cewa, "Ke fa Lantai haka kike daga zuwanki sai ki ce sai an baki to mu da muka rigaki fa ? Ta yamutsa fuska ta ce, "Yo ina ruwana da ku ban san iskanci fa."

Ai kuwa sai faɗa ya kaure tsakaninsu taga-taga sai ga Lantai ta tura wani yaro cikin ƙullun ƙosan ya kuwa ɓare  baki ɗaya.

 

Ana ihun Lantai ta zubar da ƙullu sai kuma ta ɗauki icce ta jefi wata yarinya data riƙe ta ai kuwa sai cikin kaskon man ƙosai ya kuwa zuɓe tas.

 

Mai ƙosai ta fasa ihu ta nemi kamo Lantai, Lantai kuwa ta zuba da gudun tsiya sai ga mai ƙosai ko hangen kalan kayan Lantai bata yi.

 

Sai kuwa ta nufi gidansu Lantai kai tsaye tana zage-zage tana sai an biyata kuɗin ta tas bata yadda ita.

 

Malam Muntasir yana fitowa bai zame ko ina ba sai gidansu Lantai.

Ya iske Inna Kande zaune ta zuba uban tagumi kamar kuka take yi ma.

 

Yayi sallama tayi sau uku kafin ta zabura ta nemi rugawa cikin ɗaki.

 

Sai da yayi mata magana ta dube shi ta gane shi sannan ta sauke ajiyar zuciya ta zauna.

 

"Inna lafiya kuwa ? Cewar Muntasir .

 

"Uhmmn ina fa lafiya Lantai na son kashe ni da tashin hankali ?  Cike da damuwa ta bayyana masa abin da ya faru jiya.

 

Nan take ya gano bakin zaren wato Lantai ta tura aka ɗauko mata littafin kenan ? Lallai akwai aiki gabanshi kuwa...

 

"Ina kike Kanden ? Wallahi Tallahi ba zan yadda ba ƙwandala ba zan ɗau asarar taba wallahi na sha rantsuwa ban kaffara."

 

Mai ƙosai ce ta shigo yara na biye da ita ɗuuu.

 

Daga Inna Kande har Malam Muntasir sai suka dinga kallonta yadda take masifa tana kuka.

 

Inna Kande ta dubeta ta ce, "Hure lafiya kike tafe kina sababi ?

 

Hure mai ƙosai ta ce , "Babu fa lafiya tunda Lantai tai min ɓarna nasha rantsuwa kuwa ban yadda ko ki biyani ko mai gari ya rabamu yau."

 

Inna Kande ta zaburo itama jin abin da aka ce wai Lantai ta zubar da mai da ƙullu.

 

"Ke Hure dama kin kama kanki babu sisin da zan baki ai haka sana'a take yau samu gobe rashi."

 

Malam Muntasir ya dakatar da su ya tambayi nawa ne kuɗin ?

 

Hure ta karkace tayi lissafi harda na banza ya fito da kuɗin ta ya bata .

 

Inna Kande taita masifa wai tasani bata amshi banza ba dole ta maido cikon kuɗin ai basu kai haka ba.

 

Shi dai Malam Muntasir ya samu Hure ta tafi ya dinga ba Inna Kande haƙuri.

A ranshi yana mamakin Inna Kande  yadda take goyon bayan Nuratu bayan yanzu ta gama gaya ma shi yadda ta so kasheta.

 

Ya jira zuwan Nuratun amma bata zo ba don haka yayi sallama da Innar ya tafi kada yayi rana sosai.

 

 

Ko ina Nuratu ta ruga ?

 

Ya za su kaya da Inna Kande idan ta dawo ?

Wane mataki Malam Muntasir zai ɗauka akan Nuratu ?

 

 

Haupha