ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 25

ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 25

ANA BARIN HALAL....

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*


*PAGE* 25

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559


**********
Kaman jira yake ta ambaci sunan kuma sai ga shi sun shigo tare da ummin mu, fuskan ummie a ɗaure ta nemi wuri ta zauna, gefe ɗaya kuma yayah umar ma ya zauna a gefen ummin mu, "ummie tou ke ina ruwanki da wani shiga abun da bai shafe ki ba? Ki barsu kawai Abba ya ɗauki duk matakin da yaga zaiyi dai-dai".
Ajiyan zuciya ummie tayi cikin rashin jin daɗi tace,  "ita hauwa hankali ne bata da shi, amma yaran ae abun tausayi ne, yanzu yaushe akayi auren da har duka zai fara shiga? Ni wallahi habiba tausayi ta ke bani, kuma zan nemi ita mummyn Aliyun muyi magana, meye laifin ita habiban da zata bari haka yana faruwa"?  Da sauri yayah umar ya riƙo hannun ta da ta ke shirin ɗaukan wayanta yace,  "haba ummie na don Allah kada ki fara yadda Abba yace, wallahi duk abinda ya biyo baya kanki mamie zata mayar, ki fita sha'aninta da ƴaƴanta, ae dai kinji mai Abba yace, tou babu ruwanki naki ido ne kawai".
   Shiru ummie tayi tana kallon mu ɗaya bayan ɗaya, chan kuma tace , "Allah ya kyauta",  sannan ta miƙe tayi hanyar ɗakinta, tana shigewa hafsy ta ƙyalƙyale da dariya, ƙasa-ƙasa ta shiga korowa yayah umar labarin abubuwan da ya faru, dariya sukayi tayi har suka ban haushi, ganin zasu ƙara ɓata mun rai kawai sai na fita na wuce side ɗin ummah, ina fita suka sake kwashewa da dariya da ƙarfi don naji.


Ranan da aka sallami habiba mamie tayi niyyan wuto wa da ita gida, amma fir Abba yaƙi amincewa, bada son ranta ba aka wuce da habiba gidan ta, Abba kuma ya hana raliya zuwa, ita mamin yace bazata zauna ba, idan har ta damu da aje a kula da ƴar tou ta nemo wata ƴar'uwarta ta aika, haka kuma dole tayi,
Umman ta ƙanwar mamanta ta ɗauko ta, tunda ta dawo gida ta fara sauƙe mana habaici iya son ranta, ganin abun zaiyi yawa mamah ta fito ta taka mata uban warning, babu yadda ta iya tayi shiru, ganin tana cikin damuwa ta shirya ta tafi Abuja wurin Abba, raliya kuma ta haɗa kaya ta wuce gidan ƙanwar mamin, dama duk wacce taga zataje Abuja wurin Abba baya hanawa, yawanci ma ita da mamah ne suke yawan zuwa, ita ummien mu sai ta ɗauro ko zataga likita tukun take zuwa, haka dai muka samu gidan yayi shiru na tsawon sati biyu kafin suka dawo tare da Abba.

********
Muna ta shirin fara rubuta exams yayah Ahmad ya ƙira ummi yace idan anyi hutu zaizo ya ɗauke ni, ummi ƙin amince mishi tayi, amma da taji Aunty jeeddah ce babu lafiya sai ta amince, M.G kuma rana ɗaɗɗaya ne bamu waya da shi, gashi munyi wani kyakkyawan sabo da shi, dana tambaye shi ya cigaba da bani labarin daya fara bani sai ya ƙi, yace sai ranan da yazo bauchi tukun, sannan tun ranan bamu sake hiran A.G ba da shi, gashi ina son tambayan shi yayah jikin A.G amma na kasa.
  Ranan laraba muka gama rubuta Exams ɗin mu, Alhamis kuma su hafsy suka gama rubuta neco, sai wani falli suke ji da shi, mu kuma mun gama level 2 sai shirin shiga 3, sannan a wannan lokacin ne aka saka ranan auren fatima, itama hadiza ana shirin zuwa neman auren ta, murna kaman zamuyi yayah muke ji.
Friday yayah Ahmad yazo bauchi tare da Abba,  zuwan sune mukaji labarin wai za'a zo gaisuwan auren raliya da wani ɗan ƙawar mamin ta, abun ni mamaki ma ya bani, haka kuwa akayi ranan saturday suka zo, kuma a son ransu sunso a saka musu rana , amma Abba yaƙi amincewa da buƙatan su, yace gaskiya sai ta shiga university za ayi, babu yadda suka iya haka suka yadda.
 Washe gari sunday muka kama hanyan Abuja, da yake da mota yayah Ahmad suka zo da Abba, don  ba kasafai Abba yake bin jirgi ba, yafi tafiyan mota ko dan yayi saye-sayen tsaraba, parlon Abba muka shiga yi mishi sallam nida yayah Ahmad, a can muka tarar da mamah da mamie a zaune, daga gani kuma wani abunne ya haɗasu Abba ya nemi su, don muna shiga na tsinci muryan mamah na cewa Abba yaja kunnen matar shi, banji me yace ba muka shigo, kuma sai duk suka dakata da maganan suka dawo da kallon su kanmu, gefen Abba naje na ɗan tsuguna ina ƙara gaishe shi, hannu ya saka ya dafa kaina, "sisto na har an fito za'a yi himmah ko"?  ɗaga kai nayi alaman eh, fuskana ɗauke da murmushi, domin Abba ne ya fara saka mun sisto, kafin habiba ma takama, da yake sunan sister shi naci, "Allah ya tsare hanya Ayshaa kuma don Allah idan anje ko ina kada a chanja hali da tarbiyan da muka baku, a ko'ina kuke ku nuna ko jinin Usman ne, kuma don Allah a zauna lafiya da matan yayun ki, kinga dai yadda mahaifiyar ta ke zaune da mutane? So plz kuma duk inda kuke haka nake so, Allah yayi albarka ya kawo mazaje na gari",  ya idasa faɗa yana ciro kuɗi a aljihun shi masu yawa yana miƙo mun, itama mahma nasihar ta mun, sannan ta dubi yayah Ahmad tace,  "duk zaman lpyn da zai biyo baya daga gidan ka kaine, idan ka mutunta matar ka ƴan'uwanka su mutunta ta, idan ka wulaƙanta ta su wulaƙantata, idan ka nunawa matarka ƴan'uwanka suna da daraja ta mutunta su, saboda haka kai zan jawa kunne don munga iya gudun ludayin muhammadu naka ne bamu gani ba, kaga dai yadda yarinyar nan Bintu take naknak da ku, tou daga muhammadu ne, shima kuma bai bari anci mutuncin matar shi ba, kaima sai ka kiyaye,"  godiya yayah Ahmad ya mata sannan muka musu sallama gaba ɗaya muka miƙe, tsaki mamie taja tana faɗin "halan miji zakije nema mata a Abujan ko?  Tou nema mata miji mana tunda kaf bauchi an rasa me tayawa".
"Wuce ku tafi malam Ahmadu Allah ya tsare hanya, Ayshaa idan rabon yana Abuja Allah ya kawo mana babban rabo wanda zai kai ƴan baƙin ciki masu ciwon hassada makka",  mamah ta faɗa tana bin mu da murmushi kaman bata faɗi wani abu zuwaga mamie ba, nima murmushin nayi na juya muka fita, ina kallon yadda Abba ya zubawa mamie uban harara kuma daga gani jira yake mu fita ya dirarmata,
Sai wuraren ƙarfe biyar muka isa, yayah ne ya tayani ɗaukan kayan muka shiga side ɗin shi, bamu samu Aunty j a parlor ba, ɗakinta na wuce yadda yayah ya umurceni, ina shiga kuwa na ganta dunƙule akan sallayan da tayi sallah tana bacci, ganin haka na ajiye troley nah a gefe, sannan na fito a hankali na tattara ledodin da ummie ta haɗa musu tsaraban bauchi na shige da su kitchen, ina fitowa kuma na haɗu da yayah Ahmad shima ya fito daga room ɗinshi zai shiga na Aunty j, cikin sanyin muryar shi yace, "ɗauki na gida yayah muhammad ki shigar musu da shi," da sauri kuwa na ɗauka nayi gaba, tsaban ɗokin naje naga Aunty da Areefh, don nasan fatima bata iso ba don munyi chatt tace mun sun gama Exans, amma sai ta ɗan huta zata zo, har na zolayeta kodai kabir zai shigo ƙasan ne ya sa bata taho ba, dariya tayi tace ae idan kinga kabir ƙasan nan tou ki fara shirin miƙa ni, dariya mukayi tayi ina zolayanta.

Ina shiga kuwa na haɗu da Areefh yana buga ball a parlon su, gefe ɗaya kuma yayah muhammad ne ke ta aiki a laptop ɗinshi, six month banga Areefh ba, amma da yake muna yawan video call bai manta ni ba, sake ball ɗin yayi da gudu yayo kaina, shima yayah muhammad ajiye aikim da yakeyi yayi ya ƙura mana ido yana murmushi, bayan na ajiye kayan hannu na da sauri na tare Areefh na rungume shi muna ƙyalƙyala dariya, yana rungume a jikina na wuce wurin yayah muhammad, rungumeshi nayi ina dariya, shima dariyan yake ya rungumo ni tare da areefh yana oyyoyoooo bestyn yayah, muna haka Aunty B ta fito daga kitchen tana,  "maraba da maman areefh, bestyn Baby na, dukkan mu dariya mukayi saboda Aunty B idan taso ta iya barkwanci, ajiye areefh nayi na ƙarasa wurin ta nayi hugging ɗinta, dukkan mu cike da farin ciki muka taho parlon muka zauna, gaishe su nayi suma suna tambaya na su ummie da su mamah, yayah muhammad yana tambayan ina hajiya ummah daro? Dariya mukayi saboda tuna last month da yayah yaje dagewa tayi sai ta biyo shi taga su Aunty B, wai ae mugunta ne tunda ya mayar da su Abuja yaƙi kawo su, ita zata saka a maida shi lagos ɗinshi su kuma su dawo nan kusa ya fi mata, da ƙyar aka lallaɓa ta akan zasu zo hutu ae kwanan nan, dariya mukayi sosai, Aunty ta miƙe zata koma kitchen nima sai na miƙe, juyowa tayi ta harare ni, "koma ki zauna ki huta ke da yayanki ku ƙara gaisawa, nima na kusa gamawa, jeeddah ce wai ke son cin miyar ɗanyar kuɓewa shi yasa kika ganni iwar haka a kitchen,"  murmushi nayi na koma na zauna muka cigaba da hira da yayah na, a haka kuma yaya Ahmad ya shigo suka gaisa, shima wuri ya samu ya zauna yana rungume da Areefh, hira suka fara na yadda maganan neman auren raliya ya taso suke yi, inda yayah muhammad ya juyo yana tambaya na ko akwai wanda muke tare ne? Girgiza kai nayi alaman a'a,  "babu komai kar kisaka wani damuwa a ranki kinji besty, shi aure lokaci ne, kuma duk surutun mamie kada ki bari ya dame ki, insha Allahu mijinki special yana nan tafe, ki dage kiyi karatun ki kawai, daga ke har hafsy insha Allahu zakuyi aure na mutunci,"  yayah muhammad ya faɗa, yayah Ahmad yana jijjiga kai alaman haka ne, nan ma yayah Ahmad ke cewa, "nawa ma suke ne, yanzu ne fa zata je level 3, hafsy ko yanzu ne ma suka gama ss 3 ɗin, just 17yrs ne fa, Aysha suna 20yrs, gaggawa ne kawai irin na mamie har take waƴannan surutan, ni dai nacewa ummie kada ta ɗaga hankalinta, komai zaizo a lokacin da Allah ya hukunta, "
"Hakane Ahmad, ae tun jiya da Abba ya gaya mun abun da ke faruwa na ƙira ummin har nace mata idan taga hankalinta zai tashi ta biyo Abba ta taho Abuja ta kwana biyu, amma taƙi wai kula da hajiya umma, ga umar ya gama service yana gida", cewar yayah muhammad, hira suke tayi nidai ina sauraran su rabin hankali na kuma yana tare da Areefh, a haka har aka ƙira magrib suka fita sallah, idan kin gansu kaman wasu ƴan biyu, don su ina ga ko abokai da baka ganin su tare sai junan su, ban taɓa ganin wa da ƙani da suke so close irin su ba, ko abun da ya shafi office gidajen su tou da junan su suke hiran, don da ku zuwa hira yayah muhammad zai tafi maiduguri tare suke zuwa kaman wasu aboka ne, kodan halin su yazo kusan iri ɗaya ne oho, amma banda nida hafsy, ayi shiri ayi tsiya, don ma mi bana kula tane, amma yanzu naga abun yafara mata sauƙi, tana yawan bibiyata muyi hira, ko tsakaninta da yayah ishaq ni take zuwa tayi shawara da, tom ɗinta an samu ɗan matsala ko sai daga baya?
Side ɗin yayah Ahmad na tafi ɗauke da Areefh a hannu na, ina shiga na haɗu da Aunty jeeddah tana fitowa daga ɗakin yayah Ahmad, da murmushi ta tarye ni, ni kuma naje da sauri na rungumeta, bayan mun gaisa ta tambaye ni su ummie sai na wuce ɗakin ta nayi sallah, na idarr ina askhar sai gata ta shigo hannun ta ɗauke da kilishin da ummie ta saya mun, stool ɗin dressing mirrow taja ta zauna, ina ganinta har wani lumshe ido takeyi tsaban daɗin kilishin da takeji, sallaman Aunty B ne ya sakani fasa tsokanan da nake da niyyan mata, ita ma Aunty B ɗin bakin ta ɗauke da murmushi tace,  " kai jeeddah anya tuwo na zai samu wurin shiga kuwa? Naga alaman kwantai zaiyi yau tunda an samu kilishin bauchi,"  murmushi Aunty j tayi, "Aunty wallahi yanzu na na shigo na tura ayshaa karɓo mana tuwon ne, sai naga tana askhar".
Dariya Aunty B tayi tace, "tou ku fito parlon na shigo da abincin, chan su Abu areefh suna cin nasu kada mu damesu, naga hira yau sukeji da shi, ko sunyi sabon kamu ne suke irin wannan ƙus-ƙus ɗin yau? Don naga suna ganina suke chanja topic".
Zaro ido waje Aunty j tayi, "haba Aunty ae ko ke bakici a miki kishiya ba ballantana ni da cin amarcin ban fara ba, kawai dai wani hiran su ne na daban da basu gamawa suke yi",  dariya Aunty B ta kwashe da shi ina tayata, don ganin yadda Aunty j ta wani lanƙwashe kai kamar zatayi kuka, "waya gaya miki muma mum fara cin amarcin mu? Me ma akayi? Hala ma har ku gama na ku akawo amaryah ni bamu gama ba", Aunty b ta faɗa tana juyawa zuwa parlor, bakin ta ɗauke da dariya, da sauri Aunty J ta rufa mata baya tana, "haba Aunty ki dena irin wannan wasan, nifa ko hiran za a ƙara aure bana so ballantana aje ga batun za'a mun kishiya, Allah dai ya tsare mu da ita,", ta faɗa tana jan kujeran dinning ɗinta tana zama, muma zaman mukayi muna dariyan Aunty J, a haka muka gama cin abincin na tattare nayi side ɗin Aunty B na barsu zaune a parlor suna wani hiran daban, tattare wanda su yayah suka gama ci nayi na wuce kitchen duk na wanke su, mopping na sakeyi na fito parlon, ɗago kai yayah muhammad yayi yana kallona fuskan shi cike da murmushi, "hajjaju makkatun, ƴar Abba da ummie jikar ummah, ƙanwar Muhammadu da Ahmadu Adda da ummaru da habiba, yayar raliya da hafsy ikon Allah" dariya muka kwashe ni da yayah Ahmad, gefen shi nazo na jingina ina dariya, shima dariyan yayi yace, "baxaki mun liƙi bane sisto"? Dariya yayah Ahmad yayi yace ae kuwa kachi liƙi, da dollers ma kuwa zan maka",  yana rufe baki wayana ya fara ƙara, da sauri na duba screen ɗin sai naga yayah M.G ne.


*AUNTY NICE*