WATA UNGUWA: Fita Ta 36

WATA UNGUWA: Fita Ta 36

BABI NA TALATIN DA SHIDDA

 

Maheerah da Sorfina sun kammala shirinsu tsaf don farautar rayuwar Jafsee.

 

A wata ranar Lahadi suka kira wata ƙawar harƙallarsu Maisha. Maisha ƙawa ce sosai a wurin London girl shi ya sa Maheerah bata yi tantama a kanta ba, ta amince cewar za ta iya wannan aikin ba ha'inci.

 

Maheerah ta yi amfani da tsohuwar lambar Jafsee da ke cikin layinta bata goge ba, bayan ta kira ta ji muryarsa ta tabbatar da cewa har yanzu yana amfani da ita.

Ta gyara zama sosai a kan kushin ɗin da take zaune tana fuskantar Maisha ta ce

 

 "Sister da ma mun kirawo ki nan ne saboda wani aiki da nake so ki yi mini, Sis ta yi mini bayaninki shi ya sa ba ni da wata tantama a kanki."

 

Maisha ta nutsu sosai tana sauraren Mahee luv, Mahee ta ci gaba da magana cikin yanayin ba wasa.

 

"Akwai wata lamba  da zan baki zaki saka ta a wayarki, ina so ki bibiyi mai lambar sosai. Ban san ya zaki yi ba amma ina so ne ki jafko zuciyarsa cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da kin bar masa wata kafa da zai iya zargin cewa turo ki aka yi ba.

Ki fito masa a yarinyar kirki kamilalliya mai kamala, domin shi ba ya son yin harka da gogaggun 'yan bariki, yafi son waɗanda shi ne zai janyo su a cikin harkar sannan a hankali ya ci moriyar Ganga ya yada korenta."

 

Ta ɗan tsagaita tana yin murmurshi mai ciwo, da alama ta tuna wani abin takaicin game da shi ne, sannan ta ɗora

 

"Abu ɗaya nake so da ke shi ne ki san yadda za a yi ki janyo shi zuwa nan garin, sauran abin da zaki yi zan faɗa miki daga baya."

 

Maisha ta yi wani shu'umin murmushi kana ta ce "Ai kuwa zan aikata, ki ba ni nan da sati biyu zan tabbatar masa da cewa bariki iyawa ce."

 

"Zaki iya a sati biyu kuwa? Bana so ki saka mini rai ga cimma muradina da wuri abin ya zo bai yiwu ba."

 

London girl ta yi gyaran murya kana ta ce "Zan sako baki a zancen nan, Sis Mahee ki sani Maisha gogaggiya ce, ƙwararriya ce, shahararriya ce a bariki, duk wani tuggu da kika sani ba kalar wanda bata iya ƙullawa ba, kuma tunda har ta ce miki sati biyu ba shakka za ta cika kan lokaci."

Maheerah ta yi murmushi ta ce "To ai shike nan, Allah Ya kai damo ga harawa."

 

"Ko bai ci ba ya wawwatsa ta." Cewar Maisha. Suka saka dariya su duka ukun, sa'annan Mahee ta ba wa Maisha lambar, Maisha ta yi musu sallama ta fita a gaggauce.

 

Ta bar su a zaune kowaccensu da abin da take saƙa wa a ranta.

 

'Sai na tozarta ka Jafsee, sai na fitowa duniya da asirin da kake rufewa, zan yaye wa iyayenka bargon kamalar da ka lulluɓa da shi domin su san kalar abin da suka haifa suke alfahari da shi.'

 Mahee ke wannan zancen a ranta, yayin da Sorfina take cewa a ranta

 

 'Wannan kyakkyawar dama ce ta zo a gare ni, kun yi shuka a idon makwarwa, da sannu zan bi na tone shukar na lalata amfanin gonar don na ribata da samun nasarar samun abin da kike neman ƙwace mini Mahee.'

 

A ɓangaren Irfan kuwa har zuwa lokacin yana ta fafutukar neman Maheerah bai taɓa gajiyawa ba dai-dai da rana ɗaya har zuwa lokacin da ta cika shekara ɗaya da ɓata.

Iyayensa ba yadda ba su yi da shi ba a kan ya haƙura ya auri ɗaya daga cikin 'yanmatan da ke ƙaunar shi amma ya ƙi, zuciyarsa ta yi mugun sabo da soyayyar Maheerah.

 

Dole suka haƙura suka zubawa sarautar Allah ido, a cewarsu kallo ba ya buwaya ko daga kwance ana yi.

 

Kusan duk bayan wata ɗaya sai ya karɓi wasiƙar da bai san mai kawowa ba, amma ya san mai turowar masoyiyarsa ce Maheerah domin duka sakunan haka suke nuna wa, saboda tana saka sunanta a ƙarshen kowanne saƙo. Hakan ya rage masa raɗaɗin begenta da yake.

 

Sai dai ganin ya kasa samun damar mayar mata da martanin wasiƙunta, kuma bata rubuta address ɗin da zai same ta ba, ya saka shi ci gaba da nemanta. Zuwa lokacin ya samu nasarar samo tsohon hotonta ya kai gidan jarida kamar yadda ya yi musu alƙawari.

Ba tare da ɓata lokaci ba tashar suka fara haska sanarwar nemanta.

 

******

 

Watarana da yamma tana zaune a kan gado a hotel tana taje kanta, tsohon hotonta ya bayyana a makekiyar screen tvn da ke manne a bango ana haska sanarwar nemanta.

 

Ta zazzaro idanu.

'Waye ya kai sanarwar nemana? Baba ne ko yaya...?'

Kafin ta gama zancen zucinta ta ji an ambaci sunan Irfan a matsayin wanda za a iya tuntuɓa kai tsaye idan an gan ta.

 

Sai ga hawaye 'shar' sun fara gangarowa a kan kuncinta.

'Allah sarki Irfan mai yawan ƙaunata, ka yafe ni da tozarcin da na yi maka a baya, idan har akwai ƙaddarar aure a cikin rayuwata tabbas kai ne mijina sai idan kai ne ka juya mini...'

 

Bata yi nasarar ƙarasa zancen zucinta ba saboda muryar Alhaji TJ da ta ratsa kunnuwanta inda yake cewa

 

 "Mahee luv wannan da ake haskawa a tv sak kamar ke, har sunan iri ɗaya sai dai kin fi ta kiba kaɗan." Ya faɗa yana kallonta.

Ganin hawaye a fuskarta kuma ta kasa ba shi amsa ya saka ya sake cewa

 "Ko dai ke ɗin ce? Hakan na nufin gudowa kika yi daga gida?"

 

Bata ba shi amsa ba sai tattare gashin kanta da ta yi da ribborn cikin hanzari ta miƙe ta nufin gaban mirror tana ɗaura ƙaramin ɗankwalin doguwar rigar jikinta.

 

Ganin bata tamka shi ba hakan ya tabbatar masa da ita ɗin ce, dalili kenan da ya saka ya miƙe ya je kusa da ita

 

 "Da alama akwai wani dafi a cikin zuciyarki, kuma guduwarki daga gida tana da dalili mai ƙarfi. Ki faɗa mini damuwarki, ba a ɓoyewa abokin kuka mutuwa. Na yi miki alƙawarin zan wanke miki dafin da ke zuciyarki."

 

Cikin wata iriyar murya ta fara magana "Tabbas ni ɗin ce ka gani, kuma zuwana nan garin yana da dalili, sai dai wannan rufaffen sirrina ne da ba zan taɓa buɗe wa kowa shi ba, bare kuma ungulayen bariki irinka. Ba zaka iya wanke dattin zuciyata ba, fansa ta ce ni zan..."

 

Kafin ta ƙarasa rufe bakinta wayarta ta hau ɓurari, ta ɗaga a gaggauce tana faɗar "Sister ya aka yi?"

"Wata aka hasko a TV kamar ke wallahi, ko dai ke ɗin ce mutanen gida ke nema?" Sorfina ta faɗa.

 

"Ni ma na gani sister amma ba Baba ba ne, da fari na yi tunanin shi ne har na ji farinciki yana ratsa ni, sai daga baya na gano ina yaudarar kaina ne, Baba ba zai taɓa nemana ba." Ta yi zancen cikin sanyin murya kamar mai shirin yin kuka.

"To shi mai nemankin nan waye shi a gare ki?"

"Irfan wani mutum ne na musamman a cikin rayuwata, sai dai ba zan bari ya same ni yanzu ba. Am! Sister bari gani nan zuwa gidanki na same ki sai mu yi maganar."

"Bana gida, ki same ni a wonder land park."

"Shi kenan sai na ƙaraso." Daga haka ta ɗebi wayoyinta ta saka a jaka sannan ta fice daga ɗakin ba tare da ta tamka Alhaji TJ ba.

 

Ta ja motarta a sanyaye ta nufi wonder land tana tafe tana tunanin Irfan da ƙaunar da ya nuna mata har ma da irin cin kashin da ta yi masa a baya.

 

 A kan wani babban titi ta buga motarta a jikin ta wani bawan Allah ba tare da ta ankara ba har ta fasa masa fitilar baya.

 

Cin birki ta yi ta tsaya cak yayin da matashin ya fito daga mota yana masifa. A sanyaye ta buɗe murfin motar ta fito tana faɗar

 "Ka yi haƙuri bawan Allah, ban lura ba ne."

 

A maimakon ya ci gaba da rigima ko kuma ya furta kalmar yafiya a gare ta kawai sai alamun mamaki suka bayyana a fuskarsa, sai ƙare mata kallo yake yi.

 

Sai kuma ya shiga girgiza kai a ransa yana faɗar 'Ina kai! Wannan ba ita ba ce, wannan tafi jiki waccen kuma tafi kamala. Ya ma zan haɗa waccan mai sanye da hijabi da wannan da take yawo kamar a tsirara? Wannan fa duk yadda aka yi karuwa ce.'

ko da ya dawo daga duniyar tunani tuni Mahee ta ja motarta ta yi tafiyarta.

 

 

******

A ɓangaren Sofi kuwa abin ya fara yi mata yawa kusan wata biyar kenan tana abu ɗaya, amma har yanzu ba alamar nasara kamar yadda ƙawarta ta faɗa mata. Ga bashi ya yi mata yawa.

Ga shi kuma ta yi wa kanta alƙawarin daina rayuwar shashanci don kuwa gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.

 

Don haka ta shirya ta je gidansu ƙawar tata, bayan sun kaɓe ƙawartata ta kalle ta.

"Miye damuwar kuma Sofi? Na sani tunda kika zo nan akwai damuwa don kuwa banza bata kai Zomo kasuwa."

 

"Haka ne Meerah, wato al'amarin Irfan ne na rasa yadda zan yi da shi, ga shi dai wutar ƙaunar shi sai daɗa ruruwa take yi a zuciyata, amma har yanzun ya ƙi waiwayo ni.

Na yi amfani da shawarki, kuma dukkannin wasikun da kike rubuta mini da sunan masoyiyarsa na aika masa su ina da tabbacin ya karanta, amma har yanzu bai neme ni ba."

 

Meerah ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ki daɗa haƙuri kaɗan, nan gaba kaɗan zan haɗa muku ganawa da shi ta hanyar rubuta masa wasiƙar da za ta rikita shi har ya faɗa komarmu.

 Ba zamu yarda ya gano ke ba ce har sai bayan ɗaurin aurenki da shi, kin ga daga nan ba yadda zai yi dole ya haƙura ya zauna da ke."

 

Sofi ta yi ƙayataccen murmushi "Taya kike ganin zai yi aure ba tare da sanin wacece amaryar ba?"

 

"Zai yiwu ke dai kawai ki yi duk abin da na faɗa miki, da sannu zai faɗo komarmu."

 

Waɗannan zantukan na Meerah sun sama mata sallama a zuci, don haka ta yi mata godiya ta juya a gaggauce zuwa gida, gudun kada Baba Mudi ya dawo bai same ta a gida ba.

 

UMMU INTEESAR CE