Matsalar tsaro: Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya a Sakkwato

Matsalar tsaro: Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya a Sakkwato
'Yan bindiga da ake kyautata zaton Lukurawa ne sun kai farmaki a garin Kalenjeni mahaifar shugaban karamar hukumar Tangaza Isa Kalenjeni a jihar Sakkwato.
A tabakin shedun gani da ido ya ce harin an kawo shi jin kadan shugaban karamar hukumar na barin garin.
Ya ce 'yan bindigar suna harin shugaban ne amma ba su samu nasara kan sa ba in da ya tsallake rijiya ta baya.
Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan Sakkwato DSP Ahmad Rufa'i ya tabbatar da harin ya ce hadin gwiwar jami'an tsaro sun farmaki maharan.
Ya kara da cewar sun yi nasarar kwato wasu dabbobi da 'yan bindigar suka sace suka shiga cikin dajin Tangaza.
Kokarin magana da shugaban karamar hukumar bai yi nasara ba domin wayarsa ba ta shiga a lokacin hada rahoto.
Harin ya biyo bayan gudanar da irinsa a Talata in da Lukurawa tare da 'yan bindiga a hade sun kashe mutum daya Salihu Isiyaku Hamza kuma suka tafi da dabbobi a kauyen Saminaka a yankin Tangaza.
Batagarin sun yi harbi ta ko'ina in da suka sace shanu masu yawan gaske hadi da Tumakai da Rakumai da shanu sun tsre da su a dajin Gohono.