GOSHI: Fita Ta Biyar
GOSHI
_*MALLAKAR*_
_*Umma Yakubu Imam(Maman Dr)*_
P-5
Ko da Adda Hauwa ta ƙaraso cikin ɗakin Awilo da ke kwarma ihu yana kaiwa bangon ɗakinsa duka da uban tilin bargo da kayan da ya kimawa kansa yana faɗin, "Ba, ba, ba, baaaa! ko'ina a ɗakin kayane barbaje kamar ɗakin tsohuwar mahaukaciya. Kiran duniya da Adda Hauwa ke yi wa Awilo shi bai ma san tana yi ba domin gabaɗaya hankalinsa baya jikinsa ban da ihu da ba, ba, ba, ba ya gane komai har Adda Hauwa ta ƙaraso wajensa ta riƙeshi gam tana jijjigashi haɗe da kiran sunansa na yanka "Hamza! Hamza!! Kai Hamza!!!"
Awilo dai tuni ya antaya duniyar firgici da ƙyar Adda ta iya janyoshi har tsakar gida ta duƙar da shi amma yaƙi duƙuwa yana tsaye ƙiƙam tamkar wani sabon soja a fagen fama. A tsaye Adda ta samu nasarar yakice masa tilin bargo da kayan da ya zubawa kansa, ya yin da ta nufi randa cikin sauri ta kamfato ruwa a moɗa ta zo daidai fuskarsa da ya rufe idanun gam ta sheƙamasa gabaɗaya. Tamkar ƙiftawar ido da buɗewa Awilo ya sauke wata gwaggwafar ajiyar zuciya mai nauyi kafin da bisani ya buɗe ido ya kuma rushe da wani irin rikitaccen kukan da ka ji kasan daga cikin ƙassan zuciyarsa ya tumfayo sarari.
"Adda!!!
Awilo ya furta bayan ido huɗun da ya yi da Adda Hauwa da ta haskeshi da fitila tana tofa masa addu'o'in da duk suka diro bakinta har ta samu Awilo ya yi zaman dirshen a ƙasa cikin kuka da shassheƙa. Add Hauwa dai ta cigaba da tofeshi har aka kira sallar asuba kiran farko aka fara bubbugo ƙofar zauren gidan da sai da Awilo ya zabura tare da ruƙunƙume Adda suka nufo zaure tare yana juye-juye Adda Hauwa kuma na tambayar waye?
"Ni ne Munkaila mijin Salame Adda tun cikin dare muka jiyo ihu to na bari ne a yi kirin farko na asubahi na fito Allah ya sa dai lafiya? "Hmmm" Adda Hauwa ta fara furtawa kafin ta cigaba da cewa, "Bari kawai Munkaila Hamza ne babu lafiya tun cikin dare ya yi gamo, ka ganshi ma a ruƙunƙume da ni na zo buɗe maka ƙofa. "Subhanallahi! Abin har ya kai ga haka? Cewar Munkaila Adda Hauwa ta buɗe ƙofara ya shigo ganin Awilo na kuka wiwi a ruƙunƙume da Adda ya sa Munkaila ruƙoshi sosai suka ɗunguma zuwa cikin gida. Daga haka kusan maƙotan Adda maza da mata suka cika gidan fal aka zaunar da Awilo a tsakiya bayan tofe-tofe da shan rubutu har da su turare da aka yi masa kuma zazzaɓi me zafi ya lulluɓeshi. A nan dai Adda ta ɗauko waya hankali a tashe ta bawa su Munkaila a kira mata Baffa domin ta sanar da shi abin da yake faruwa, daidai lokacin Goshi ta danno kai cikin gidan riƙe da kayan makarantarta da jakarta a rataye. Da sauri Goshi ta ƙaraso ko gaisuwar safiya bata yi wa kowa ba ta fara tambayar Adda Hauwa da cewa, "Adda me ya faru da Awilo na gan shi raɓe-raɓe a kwance yana rawar ɗari?
"Ai ke dai bari Goshi Allah ya ƙaddara ba zaki ga tashin hankalin da na gani ba tun daren jiya Hamza ke fama har asubahi da su Munkaila suka shigo suka taddamu gashi har yanzu ma mutanen ba su sakeshi ba. "Mutane kuma Adda? Su waye suka kama Awilon?
"Mutanen ɓoye mana Goshi, su suka bugeshi tun daren jiya duk da tofi da rubutu haɗe da turaren da bayin Allah nan suka yi masa amma har yanzu don zalinci ba su barshi ba, kin ga ba wannan ba maza ki sanya kayan makarantarki ki wuce ki tafi kar ki makara na san ai kin yi karin-kumallo a gidanku ko? "Allah ni babu abin da na ci Adda ko koko baki dama ba? Ya Ilahil alamin, ana ta kai Goshi wayake ta kaya, a ina zan samu zarafin dama wani koko ballanatana kunu? Ki wuce ɗaki ki ɗauki wazobiya ko ɗan malele ko shasshaka kya siya ki ci a can kin ga baffa kar ya zo ya sameki a nan baki wuce makaranta ba.
"To!
Goshi ta amsa haɗe da fakar idon Adda Hauwa ta yi wa Awilo gwalo da ke kwance yana rawar ɗari gabaɗaya duk ya yi zuru-zuru tamkar muzuri ya kama ɓera. Goshi ba ta kuma tankawa Adda Hauwa ba ta shiga ɗaki ta ɗauki wazobiya ta fito bayan ta sanya kayan makaranta ta rataya jakarta wata yarinya ta shigo gidan sanye da kayan makaranta ta gaida Adda da sauran mutanen da ke wajen. Cike da mamaki Adda Hauwa ta dubi yarinyar ta ce, "A'a su Saude ne yau a gidan nawa har an biyowa mutuniyar makaranta, yaushe kika san ta zo wajena? Saude na dariya har za ta buɗe baki ta yi magana Goshi da ke tafe ta ce, "Tun jiya da aka taso mu daga makaranta na gaya mata fa na dawo gidanki Adda. "To na ji maza ku kama hanya ku tafi, don Allah ban da faɗa da ciye-ciye a hanya kun dai ji ko?
"Mun ji Adda.
Goshi ta furta suka fito tare da Saude ƙawarta da yake gidansu babu tazara me yawa tsakaninsu da gidan Adda Hauwa. A hanya su Goshi suka dinga haɗuwa da wasu ƴan ajin na su, wasu kuma ba ajinsu ɗaya ba amma dai makarantar su ɗaya. Tare suka ɗunguma har cikin makaranta ɗalibai na ta ƙoƙarin shiga ajujuwansu, karaf malam Bukar ya hango Goshi, da gudu ya fito daga cikin ofishinsu na malamai maza cikin hanzari ya nufosu gadan-gadan yana danƙara wa Goshi zagi me haɗe da kira kamar zai kai mata duka.
Goshi ta tsaya tsam haɗe da tsugunawa tana gaida malam Bukar daga inda take har malam Bukar ya ƙaraso wajen yana cewa, "Ƴar jakar uba ashe bakida kunya? Har kika iya takowa cikin makarantar nan yau dama shi alhaki ai kwaikuyo ne. Malam Bukar na gama faɗin haka ya tasa ƙeyar Goshi zuwa ofishin hedimasta bayan ya ƙora su Saude zuwa aji, Goshi dai bata ce ƙala ba har suka shigo ofishin hedimasta ta gaishe shi ya amsa, ya kuma dubi malam Bukar ya ce,
"To fa Allah ya kawo mu safiyar, har yaran nan sun fara saka ka magana ko malam Bukara? "Ina fa yallaɓai ka tuna Bilkisu jiya da mahaifiyarta ta kawo ƙarar wata ƴar ajinsu ta saɓa mata kamanni?
"Ƙwarai kuwa na tuna malam Bukar, kar dai ka ce mini wannan figigiyar yarinyar ce da bai wuce a tura ta a hanci ba ta yi mata jahilin dukan nan? "Wallahi tallahi ita ce yallaɓai ka ganta ƴar firit amma ta fi kowa fitina a ajinsu ga uban taurin kai kamar shaiɗaniya. "Ai kuwa duk sheɗancinta yau sai ta gane Allah ɗaya ne bashida abokin tarayya malam Bukar amso mini bulala na fara tafkarta kafin dukkan gaɓɓanta su gaya mata yau za ta san makaranta ba wajen iskanci da rashin mutunci ba ne.
"An gama yallaɓai.
Cewar malam Bukar, ya yin da ya fito jiki na rawa ya je ya samo bulalai har guda biyu ya kawo wa hedimasta ya karɓa tare da baiwa Goshi umarni ta taso daga tsugunen da take ta matso kusa ta kuma ja wandon makarantarta sama. Ba musu Goshi ta miƙe tsaye haɗe da matsawa kusa da hedimasta bayan ta tsaya ta ja wandonta sama hedimasta ya fara zambaɗa mata bulalar da ko alamun ƙwalla babu a maganan Goshi abin da ya ƙara ƙular da malam Bukar ke nan ya amshi bulalar daga hannun hedimasta a harziƙe ya fara zubabawa Goshi a ƙafa, jiki har da kan ta. Malam Bukar na dukan Goshi Bilkisu da mahaifiyarta suka danno kai cikin ofishin hedimasta don ko hedimasta bai yi musu bayani ba Bilkisu ta sanar da mahaifiyarta cewar ga Goshin nan malam Bukar na jibga. Mahaifiyar Bilkisu ta dungure mata kai da faɗin,
"Ashe dai Bilkisu girman banza gareki da har za ki tsaya ƴar figigiyar yarinyar nan ta yi miki mugun duka? "Wallahi ni kaina sai da ni yi mamakin cewar wannan ƴar abar ce ta yi wa Bilkisu wannan daƙiƙin dukan, gashi dai a girman jiki Bilkisu ta ninka ta kusan sau biyu son abin kunya. Ka ga ma malam Bukar bar bugun nata haka mu ji dalilin da ya sa ta so nakasta Bilkisu kafin mu ingiza ƙeyarta har gaban iyayenta. Hedimasta ya furta, ya yin da malam Bukar ya bar bugun Goshi wanda har haki yake tsabar dagewar da ya yi yana dukanta. Ko da malam Bukar ya tsaya da bugun Goshi, zaman dirshen Goshi ta yi idanunta jajir amma dai babu alamar kuka, ƙafafuwanta kuwa duk sunyi ruɗu-ruɗu da bulala hedimasta ya dubeta ya ce,
"Ke ya sunanki?
"Goshi... Goshi ta furta a gajarce.
''Goshin ubank ko mu sa'aninki ne. malam Bukar ya furta a fusace ya kuma zubawa Goshi bulalan hannunsa guda biyu haɗe cewa, "Sunanki na gaskiya ake tambaya don gwafar ubanki. Sai a yanzu Goshi ta saki wani marayan kuka me ɗacin zafin zagin da malam Bukar ya yi mata tare da cewa,
"Ha, ha, Hauwa Baffa sunana malam.
"Ajinki nawa? Hedimasta ya sake wurgowa Goshi tambaya akaro na biyu ta kuma amsa masa da cewa,
"Biyar.
"Me Bilkisu ta yi miki kika yi mata mugun dukan nan har kika so nakasta ta? Ko kasheta kike son yi ne Hauwa Baffa?
Cike da shassheƙar kuka Goshi ta girgiza kai haɗe da cewa,
"Ni, ni ban doketa ba wallahi malam.
@Real Maman Dr
(2025)
managarciya