Babban Buri:Fita Ta Sha Ɗaya
BABBAN BURI
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.
بسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~"Ina me gaya maku kar kuyi kuka dani!!!."
Yana gama maganar ya fice da sashen ransa a ɓace ya tabbata waƴannan kwaɗayin duniya ya rufe masu ido.
Wani murmushi Alh Bello ya yi wanda na rasa gane na miye sai can ya miƙe ya dawo tsakiyar ɗakin taron ya kalli kowa da kowa fuskarsa ɗauke da murmushi sannan ya ce "waishi yaron nan a nashi ganin zai tsoratar damu ne domin mu fasa aiwatar da ƙudurinmu?, Cabbb kar ɗaya daga cikin ku ya bari kalamansa su sanya yamai gwiwa, ku fita batunsa aure ba fashi!."
"Na dai san duk haukarsa ba zai sako mana ita ba, badan komai ba kuwa sai dan kujewa ɓacin sunan mahaifinsa duk da ya rigamu gidan gaskiya amman ba zaiso hakan ba, cox gaba ɗaya al'ummar jahar Sokoto ba wanda besan AS wurno ba, kunga kodan wannan ina sa ran bazai aikata wani mummunan abu a kan Safiya ba."
Ko wannen su ya yi na'am da maganar Alh Bello a haka taron ya watse akan a ci gaba da shagalin biki kawai.
★★★★★★
"Ni dai wallahi Allah Alh hankalina be kwanta da auren nan na Safiya da Haidar da kuke ƙoƙarin ƙullawa , gaba ɗaya dana tuna da waye zata aura sai naji gabana ya yanke ya faɗi ganin nake yi kamar wani abu marar daɗi zai faru, meyasa ba zaku canja da wata ba nikam a barmin ƴata har Allah ya kawo mata nata mijin wanda hankalina ya kwanta dashi?."
Ajiye cup ɗin daya dauka da sunan ya kai bakinsa amman jin maganarta ya sanya sa dakata , ya yi a saman center table dake kusa dashi, sannan cikin dakakkiyar murya ya ce "Lauratu"! ba tare daya jira jin ta bakinta ba yaci gaba da cewa "a karo na ba a dadi iname ƙara sanar dake ki kiyaye bakinki a kan aurennan, kisa masa albarka kawai ba wai dogon zance ba, daga yau bana buƙatar jin wani ƙorafi a gareki wanda ya dangancin auren nan."
"Na biyu batun mu bawa Haidar wata daga cikin ƴaƴanmu wannan be taso ba, domin kuwa Safiya ce kawai zata iya yi mana aikin da muke so da alamu, don haka ba wacce zamu ɗaura aurenta dashi face ita."
Gyara zamansa ya yi kana ya gurgusa kusa da'ita sosai har suna jiyo saukar numfashin juna sannan cikin ƙasa da murya ya ce "ke wannan bama abin farin ciki ne dake ba a ce ƴarki ta auri yaro kamar Haidar?, Yaro dogo fari kyakkyawa dukiya ilimi duk Allah ya bashi ,wanda duk wata mace wacce ta ɗaura wa idanuwanta akansa bata da burin komai a ranta saina mallakatarsa."
"Anya kinsan yadda matan gidan nan suke jin zafin zaɓar Safiya da a kayi a matsayin matar Haidar kwa?, dan Allah ki sawa zuciyarki salama muci dukiya dukiya dukiya!!!, ya iyar da maganar yana me wasa da hannunsa kana kuma ya kwashe da dariya.
Da kallon mamaki ta bisa tana me ayyana abubuwa da dama a ranta.
Bata gama dawowa daga duniyar tunani ba taga ya wurga ta gefenta yana faman sakin murmushi.
Miƙewa ta yi jikinta a saɓule ta nufi ɗakinta.
A saman gado ta zube tana me tunanin abubuwa da dama ciki kuwa harda rashin damuwar da mijin nata beyi da lafirar sa ba shi dai burin sa ya samu duniya dashi har ƴan uwansa, tabbas ta tabbata ko wacce rayuwa da nata Burin , sai dai su burin nasu ya ɓaci domin kuwa matuƙar zasu samu kuɗi to ba abinda ba zasu iya aikata wa ba, *"RAI DA BURI!"* ta faɗa tana me girgiza kai.
★★★★★★
Bayan ya dawo daga sallar isha'i sashen Hajiya Inna ya nufa domin gaya mata shirin nasu, tuwo ta kawo masa da miyar kuka wacce taji daudawa zallah, zama ya yi yaci ka cikinsa dashi sannan ya kalli Hajiya Inna ya zayyane mata abinda ke faruwa.
Cike da mamaki take kallonsa sannan ta ce "anya waƴannan mutanen suna da hankali kuwa?, Meyasa waƴansu mutane basa da tunani ne?" meye abin garaje a cikin wannan lamarin kuma?" ni wallahi Allah hankalina be kwanta a kan auren wannan yarinyar ba, gaba ɗaya ni basa raina da sun barka kaje can waje ka samo wacce tayi ma ba dai su suyima haka ba".
Murmushin gefen baki ya yi sannan ya ce "karki damu Hajiya Inna zan gyara masu zama ne walle, zan basu mamaki! badai sun nace da aure aure ba?, hummm barsu kawai suje suyi."
"A'a Shalele kar a zartar da hukunci cikin fushi ba, la ƙyale su kawai , Allah ya baku zaman lafiya, idan bikin ya ƙara to saura sati ɗaya ka gayamin naje can ƙauye na faɗo masu domin suma suzo ayi dasu".
"Me zaki gaya masu kuma? Sai kace auren so? Dan Allah ki nemi guri kiyi zaman ki karki wahalda kanki da kaina zanje na sanar masu kuma zan aika masu da motar zuwa biki."
"Da kyau Shalelena Allah ya baku zaman lafiya ya kauda idanuwan maƙiya a kanku".
Ba tare daya ce komai ba ya miƙe ya fice daga ɗakin.
Ɗakinsa ya nufa kai tsaye, a Parlour ya hau Safa da marwa, har yau ya rasa wanne irin hukunci ya kamata ya zartar masu game da kisan gillar da suka yiwa mahaifinsa gaban idanuwansa har yau abin ya kasa goguwa daga cikin kwakwalwar sa, runtse idanuwansa ya yi lokaci ɗaya abinda ya faru shekarun baya ya dinga dawo masa a kai, ji yake yi kamar lokacin ne abin ya faru.
"Baba Bello Baba Murtala kune kuka kasheman mahaifina!!!, Sai dai har yau na rasa gane dalilin ku nayin hakan, ko yaushe ƙanen mahaifina zai bayyana?, Ina kuka kaimin shi?, saina sanya ku kaku kamar yadda kuka sanya ni! saina sanya ku kuka kamar yadda kuka sanya Kakata wacce itace matsayin Uwa Uba a guna! tunda kuka yi sanadiyar ko nace kuke kan zubar hawayenta sai naku hawayen sunfi nata zuba! zan baku mamaki".
Ya faɗa yana me riƙe kansa na hannayensa biyu yayinda idanuwansa duka canja launi daga farfaru zuwa jawur kamar garwashin wuta.
Zubewa ya yi a saman gwiwowinsa ya yinda ya duƙar da kansa ƙasa hannayensa tafe da ƙasa yana me ƙoƙarin saita nutsuwarsa zuwa ga gangar jikinsa.
Ya jima a haka sannan ya miƙe kamar ya faɗi ya buɗe freezer dake ajiye a ɗakin ya ɗauko ruwan swan ya kafa a bakinsa.
Be ɗauke gorar ruwan a bakinsa ba sai da ya shanye ruwan kaff kana ya wurgar da gorar gefe yana me sauke ajiyar zuciya.
Uwar ɗakinsa ya shige ya ɗauko wata ƴar ƙaramar jikka ya zube abubuwan dake ciki a ƙasa kana shima ya zube a ƙasa yana me biyan photunan da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Tsayar da idanuwansa ya yi a kan photo ɗaya yana shafar fuskar photon sannan cikin sarƙewar murya ya ce "Allah ya bayyanamuna kai mahaifina, muna matuƙar buƙatar ka a gusa damu, Allah yasa duk inda kake kana cikin kwanciyar hankali.
★★★★★★
Yauma kamar kullum bayan na gama aika ce aikace na harna shirya haka A'isha ta yi shirin makarantar ta , ɗakin Mama muka nufa domin kuwa tun sallar safe bamu sake ganinta ta fito waje ba, shigarmu ɗakin muka iskota kwanci ba lafiya ciwon ciki mai tsanani ne ya rufe ta a matuƙar kiɗime na yi jifa da jikkata da nake riƙe da ita na ƙarasa gunda take kwance sai murƙususu take yi kamar wacce ake fitarwa rai.
Kallon A'isha na yi na ce "jeki masallaci ki gayawa Baba dan Allah, kice ya yi sauri A'isha kema ki hanzarta dan Allah."
Ficewa ta yi daga cikin gidan itama a kiɗime fitar ta keda wuya mama ta kalleni cikin gala baituwa ta ce "Khadeejah inaji a jikina rayuwata bamai tsawo ba ce , khadeejah ki riƙe ƙannenki kamar yadda kika saba karki bari zumuncin ku ya lala ce, Khadeejah.... Sai kuma ta tsaya sannan ta cije baki alamar ciwon hana ratsata sannan taci gaba da cewa "ki duba cikin jikkata tana cikin samiruna zaki ga........ sai kuma muryarta ta sarƙe cike da tashin hankali na fice a ɗakin na ɗobo ruwana na dunfaro ɗakin da gudu sai dai me zan gani?.........
ƳAR MUTAN BUBARE CE
Maryamah