Gamayyar ƙungiyoyin matasan APC 218 sun jaddada goyon bayan su ga jam'iyyar a jihar Yobe

Gamayyar ƙungiyoyin matasan APC 218 sun jaddada goyon bayan su ga jam'iyyar a jihar Yobe

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Gamayyar kungiyoyin matasan jam'iyyar APC 218 (COYAPO), a jihar Yobe suka gudanar da gangamin taron jaddada goyon bayan su ga jam'iyyar APC tare da cikakken goyon bayan su ga Gwamnan jihar, Hon. Mai Mala Buni da sauran dukan yan takarar da jam'iyyar ta tsayar a kowane mataki. 

Kungiyoyin sun gudanar da taron gangamin a filin wasa na makarantar Firamaren Njiwaji da ke tsakiyar birnin Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe, wanda ya samu halartar dubban matasan tare da shugabanin kungiyoyin da jiga-jigan jam'iyyar APC a shiyya ta daya (Zone A) wanda ya kunshi kananan hukumomin Damaturu, Gujba, Gulani, Tarmuwa, Bursari, Geidam da Yunusari.

 Hadakar uwar Kungiyoyin (COYAPO) wadda ta matasa ce maza da mata zallah, ta bayyana makasudin shirya wannan gangami wanda ya hada dukan matasan jam'iyyar APC a fadin jihar Yobe, domin jaddada goyon bayan su ga Gwamna Mai Mala Buni bisa kulawa ta musamman da ya bai wa matasa a gwamnatinsa kamar yadda ya yi alkawari, inda matasan suka sha alwashin ramawa kura aniuarta wajen aiki tukuru wajen samun nasarar sake zaben sa a karo na biyu a zaben 2023.

A jawabinta ga dandazon matasan, shugabar matan APC a shiyya ta daya (Zone A), Hajiya Budu Lawan ta bayyana cewa a tarihin kowane zabe a Nijeriya, mata da matasa ne ke kan gaba wajen yankar katin zabe tare da yawan adadin masu jefa kuri'a fiye da sauran kaso. Ta ce "Kuma mata sune suka fi kowa yawan a cikin masu jefa kuri'a." 

"Babu wani mai ja kan cewa mune kan gaba waken yawan masu jefa kuri'a a kasar nan, kuma saboda haka mun yi alkawari dukan kuri'armu mun sadaukar da ita ga yan takarar jam'iyyar APC, daga matakin sama har kasa. Zamu yi tsayin daga wajen ci gaba da wayar wa mata kai kan su zabi APC a jihar Yobe da Nijeriya." In ji ta.

A jawabin shugaban hadakar kungiyoyin matasan APC a shiyya ta daya (Zone A), Alhaji Babagana Alhaji Modu Goneri (Bature Goneri) ya jaddada cewa, gamayyar Kungiyoyin sun shirya wannan taron gangamin ne don hada kan matasan jam'iyyar APC sakamakon yadda harkokin babban zabe suke karaatowa saboda samun gagarumar nasara.

Bature Goneri ya kara bai wa matasan tabbacin cewa, tun a tashin farko gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni, ta matasa ce kuma ko shakka babu matasa ne suka ci gajiyar ta fiye da kowace gwamnatin da aka taba kafawa a jihar, saboda haka matasa su kara kaimin bayar da cikakken goyon baya don ya sake komawa karo na biyu, domin ya dora daga inda ya tsaya.

Har wala yau kuma, shugaban gamayyar Kungiyoyin ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, sun kammala shiri tsaf don tallafawa mata 250, kananan hukumomi 17 dake fadin jihar da turamen zannuwa da makamantan su.