Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Nisanta Kanshi Da Barin  Jam'iyar PDP

Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Nisanta Kanshi Da Barin  Jam'iyar PDP
 


Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan'iya ya nisanta kan shi da barin jam'iyarsa ta PDP.
Barin jam'iyar ya fito a wata takardar da aka fitar tana yawo a kafafen sadarwa na zamani wadda ya aika ga shugaban mazabarsa ta Kware a karamar hukumar Kware a jihar Sakkwato.
A takardar Mataimakin Gwamna ya sanar cewa ya janye shedar zamansa dan jam'iyar PDP tun da 8 ga watan Fabarairu na 2023.
Ya godewa damar da aka ba shi ya yi aiki matakai da dama a cikin jam'iyar PDP.
Darakta yada labarai a ofishin mataimakin gwamnan Aminu Abdullahi ya fitar da takardar karyata fitar mataimakin Gwamna wadda ya sanyawa hannu ya ce "hankali na ya karkato cewa Mataimakin gwamna ya bar jam'iyar PDP ba gaskiya ba ne karya ce  ta karshe. 
"Ina nan jam'iya ta PDP cikin goyon bayan jam'iyata da gwamnatin Sakkwato." a cewarsa.