Tsaro A Neja: Ƙaramar Hukumar Bosso Ta Sha Alwashin Samar Da Kundin Bayanai Kan Gidajen Haya Da Tantance  Baƙin Da Ke Shigowa

Tsaro A Neja: Ƙaramar Hukumar Bosso Ta Sha Alwashin Samar Da Kundin Bayanai Kan Gidajen Haya Da Tantance  Baƙin Da Ke Shigowa

 


 
 
Daga Babangida Bisallah, Minna
 
 
Karamar hukumar Bosso ta sha alwashin samar da kundjn bayanan gidan haya dan tantance bakin da ke shigowa ta yadda za a sanya ido akan shiga da ficen jama'a musamman saboda matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar nan.
Sakataren karamar hukumar, Hon. Garba Joeji ne ya bayyana hakan ga manema labarai, bayan cafke wadanda ake zargi da tseguntawa mahara masu dauke da makamai sirrin jama'a a karamar hukumar.
Joeji yace dole jama'a su yi hakuri da irin matakan da take dauka ganin yadda ake samu karuwar kai hare-haren ga jama'a dan yin garkuwa da su dan samun kudin fansa. Saboda haka ina kiran al'ummar Bosso da su cigaba da baiwa gwamnatin karamar hukuma, bisa jagirancin Arc. Hon. Abubakar S. Gwamna da na jiha da yake aikin kafada da kafada ake gudanar da shi dan tsare rayuka da dukiyoyin jama'a kan yadda bata gari ke kokarin sun hanawa al'umma kwanciyar hankali.
Karamar hukumar Bosso na daga cikin kananan hukumomin da ke fuskantar matsalar hare-haren yan bindiga, wanda ko a kwanakin baya sai da yan bindigar suka kawo samame a cikin garin Maikunkele inda sakatariyar karamar hukumar take, inda suka yi a won gaba da mutune biyu.
Sakataren ya cigaba da shawartar al'ummar karamar hukumar da su cigaba da sanya idanu, muddin suka ga wani abin barazana ga tsaro da su gaggauta tseguntawa jami'an tsaro dan daukar matakin gaggawa.
Gwamnatin jihar dai ta bayyana cewar kananan hukumomi ashirin da biyu cikin ashirin da biyar na jihar na fuskantar matsalolin tsaro, wanda a cewar sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Matane gwamnatin ta kashe naira biliyan biyar wajen yaki da yan ta'adda ta hanyar karfafawa jami'an tsaro da siyawa yan banga kayan aiki.