Jami'an Tsaro Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Ceto Mutane a Jihar Kebbi

Jami'an Tsaro Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Ceto Mutane a Jihar Kebbi
 
Jami'an tsaron haɗin guiwa da suka ƙunshi, dakarun sojoji, yan sanda, DSS da jami'an Sibil Difens sun ragargaji 'yan bindiga a jihar Kebbi ranar Lahadi. A rahoton da Jaridar Daily Trust ta tattaro, ya nuna cewa gwarazan jami'an tsaron sun ceto mutane uku da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a dajin Kanzanna da ke ƙaramar hukumar Bunza.
 
Jami'an tsaron haɗin guiwar sun kuma aika wani hatsabibin ɗan bindiga zuwa lahira yayin da wasu da dama suka gudu ɗauke da raunukan harbin bindiga. Wannan nasara ta samu ne biyo bayan samamen da dakarun sojojin Najeriya suka kai kan ƴan bindigan, waɗanda suka hana al'umma zaman lafiya. 
Gabanin wannan samame, 'yan bindigan jejin sun kai hare-hare masu yawa kan fararen hula a kananan hukumomin Kalgo, Bunza da kuma Arewa, PM News ta ruwaito. 
Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwa na Birnin Kebbi, AbdulRahman Usman, ya ce Gwamna Nasiru Idris ya bada umarnin tura karin jami’an tsaro. Ya ce mai girma gwamna ya bada umarnin hanzarta tura ƙarin dakarun tsaro zuwa ƙananan hukumomin da lamarin 'yan bindiga ya taɓa domin tsare rayuka da dukiyoyin jama'a.