'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutumi da Katin Zabe Sama da 100 a Jihar Sakkwato

'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutumi da Katin Zabe Sama da 100 a Jihar Sakkwato

 

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Sakkwato ta kama wani mutumi mai suna Nasiru Idris ɗan yankin ƙaramar Sabon Birni ɗauke da Katunan Zaɓe (PVC) guda 101. Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kwamishinan 'yan sandan jihar, Hussain Gumel, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai ranar Alhamis. 

Kwamishinan ya ce dakaru sun yi ram da wanda ake zargin ne a garin Sabon Birni ranar 10 ga watan Oktoba, 2022 biyo bayan samun kwararan bayanan sirri. 
Hussain Gumel ya ƙara da cewa mutumin ya gaza ba da bayanin yadda ya tattara waɗannan katunan zaɓe da garuruwan da ya haɗasu.
"Mun gano cewa masu Katin zaben ba mazauna ƙaramar hukumar Sabon Birni bane kaɗai ba, da yuwuwar masu katunan na zaune a wasu sassan jihar Sakkwato domin an gaza bibiyar asalin mamallaka katin PVCn." 
Daga nan, CP Gumel ya yi kira ga ɗaukacin al'umma musamman waɗanda katin zaɓensu ya ɓata ko suka aje a wurin da bai kamata ba da su gaggauta zuwa Hedkwatar yan sanda su diba. Yace hukumar yan sanda zata miƙa ragowar katunan da ba'a zo an karɓa ba ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) bayan wata ɗaya.