Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga a Sakkwato

Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga a Sakkwato


Dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar halaka hatsabibin ɗan bindiga mai haɗari wanda ke shigar ƴan sanda yana aikata ta'addanci a jihar Sakkwato.
 
Sojojin sun kuma lalata ma'ajiyar magungunan ƴan bindiga da wuraren kiwon lafiyarsu a wani samame da suka kai ranar Laraba 20 ga watan Maris, 2024.
Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa a X a ranar Alhamis (yau), 21 ga watan Maris.
 
A cewar Nwachukwu, dan ta’addan ya sha yin shiga a matsayin ɗan sanda wajen yaudara da yin garkuwa da mutane masu yawa da ba a san adadinsu ba. 
Sanarwar wadda rundunar soji ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis ta ƙara da cewa: "A wani samamen na daban da dakarun sojoji suka kai a jihar Taraba, sun yi nasarar kashe wani ɗan ta'adda a ƙauyen Kutoko da ke ƙaramar hukumar Takum a jihar."
 
"Baya ga haka, a samamen sojoji sun kuma kwato bindiga ƙirar AK-47 da Magazine ɗauke da alburusai huɗu na musamman masu nauyun 7.62mm."
 
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa irin wannan hare-hare da sojoji ke kai wa na ƙara tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya ta shirya kakkaɓe duk wani nau'i na ta'addanci. 
A cewarsa, wannan wani ɓangare ne na yunƙurin rundunar soji wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu gindin zama a tsakanin al'umma.