Bikin Kirsimeti: Gwamna Buni Ya tallafa wa Kiristoci 500 da kayan abinci a Yobe 

Bikin Kirsimeti: Gwamna Buni Ya tallafa wa Kiristoci 500 da kayan abinci a Yobe 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

A kokarin gwamnatinsa na ganin ta tallafa wa kowane bangaren al'ummar jihar, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ranar Jummu'a ya bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) umurnin tallafa wa Kiristoci maras galihu, zawarawa da marayu kimanin 500 kayan abinci da na masarufi domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin walwala a fadin jihar.

Shugabannin kungiyar CAN reshen jihar Yobe, Bishop Yohana Audu tare da hadin gwiwar mai taimakawa Gwamna Buni (SSA) kan kyautata alaka tsakanin mabiya addinai, Mr Emmanuel Degubi Ayuba, sun bayyana daukar ingantattun matakai wajen zakulo wadanda suka cancanta su ci gajiyar tallafin na wannan shekara. 

A jawabin Babban Sakataren Hukumar SEMA, Dr. Mohammed Goje, sa'ilin da yake jagorantar raba kayayyakin, ya yi kira ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin cewa kada su manta da makobta da yan uwansu wajen yin tarayya da su ta fannin basu wani kaso a kayan abincin a matsayin nuna kauna da haɗin kai. Tare da ba su tabbacin cewa Gwamna Bunis a shirye yake ya ci gaba da tallafa wa marasa galihu a fadin jihar.

A nashi bangaren, Shugaban CAN wanda ya samu wakilcin Sakataren Kungiyar, Rev. Abako inda ya yi addu’ar samun hadin kai tsakanin al'ummar jihar tare da fatan samun nasara a zaben 2023 mai zuwa. 

Da yake jawabin godiya ga Maigirma Gwamna, Hon. Mai Mala Buni CON, Mai Taimakawa Gwamna kan al'amurran kyautata alaka tsakanin mabiya addinai, Mr. EMMANUEL Degubi ya yaba wa Hukumar SEMA a jihar Yobe, inda ya ce "Wannan shi ne karon farko wanda a tarihin jihar Yobe Gwamnan jihar ya nada masu bashi shawara SA da SSA kimanin 13. Wanda babu abin da zamu bayyana sai lokacin zaben 2023, za mu bayar da babban tukuici." 

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun fito ne daga Kungiyoyin daban-daban a fadin jihar Yobe, wanda ko shakka babu tallafin zai rage wahalhalun da masu karamin karfi ke fuskanta, musamman a makamancin wannan lokaci na bikin Kirsimeti.