Buhari Zai Yi Jawabi Ga Mutanen Ƙasa

Buhari Zai Yi Jawabi Ga Mutanen Ƙasa

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga Ƙasa ranar Lahadi 12 ga watan Yuni 2022 da karfe Bakwai na Safiya ciki da wani bangare na girmama ranar Mulkin farar hula. 

Don haka ana bukatar da kafafen yada Labaru na Radiyo, Telabijn da sauran kafafen sadarwa dasu hada da Babbar tashar Talabijin na ƙasa NTA da Radiyo don yada jawabin shugaban. 

Femi Adesina babban Mai bawa Shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai da wayar da kan jama'a ya sanar da hakan.