Obasanjo Mutum ne mai hangen nesa da son cigaban ƙasa-- Gwamna Yahaya Bello

Obasanjo Mutum ne mai hangen nesa da son cigaban ƙasa-- Gwamna Yahaya Bello

Daga Ibrahim Hamisu.

Gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar neman shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC Yahaya Bello ya taya tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo murnar kara shekara a ranar Asabar 6- 3- 2022

Obasanjo wanda ya cika shekara 85 a duniya, Yayaha Bello ya ce tsohon shugaban kasar ya karfafa masa guiwa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kogi.

A wata takardar taya murna da Gwamnan ya aikawa Obasanjo, wanda kakakin Gwamnan Onogwu Mohammed ya fitar ya bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin mai kishin kasa da son cigaban yankin Afrika.

Dan takarar shugabancin ƙasar ya kara da cewa “Obasanjo mutum ne mai cike da basira da hangen nesa wanda ya goge wajen lamurran da suka shafi sha’anin mulki  da tsaro da jagoranci nagari”.