Tambuwal Ya Nada Sabbin Kwamishinoni Guda  9

Tambuwal Ya Nada Sabbin Kwamishinoni Guda  9

 

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya nada sabbin kwamishinoninsa guda Tara, in da ya aika da sunayensu ga majalisar dokokin jiha domin tantancewa da amincewa.

Tambuwal ya sake dawo da tsoffin kwamishinoninsa guda shida, Honarabul Aminu Bala Bodinga da Kanal Garba Moyi da Honarabul Bashir Gidado da Honarabul Salihu Maidaji da Honarabul Abullahi Maigwandu da Abubakar Mai kudi Ahmad.

Ya nada sabbi gudu uku Honarabul  Bashir Mohammed Lambara, Honarabul Abubakar Dange da Honarabul  Abdullahi Yusuf Hausawa.

 

 

Ya sake nada  Alhaji Mukhtar Magori matsayin shugaban fadar gwamnatin jiha.

 

A takardar da mai Magana da yawun Gwamna Tambuwal, Muhammad Bello ya fitar ga manema labarai ya nuna tsoffin kwamishinonin da aka sake nadawa sun ajiye ne a lokacin da za su shiga neman wasu kujeru na siyasa domin yin biyayya ga dokar zabe ta kasa.