Matashin Da Aka Soma  Yi Wa Yankan Rago  Ya Kuɓuta A Kano

Matashin Da Aka Soma  Yi Wa Yankan Rago  Ya Kuɓuta A Kano

 

Rundunar 'yan Sanda a Jihar Kano ta ce ta kuɓutar da wani matashi da a ke zargin wasu 'yan damfara sun yi yunƙurin yi wa yankan rago.

 

Lamarin ya faru ne a wani gida a Ƙaramar Hukumar Dambatta a Kano.

 
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa sun sami labarin faruwar lamarin ne bayan da matashin da aka fara yankawa maƙogwaro ya kai musu ƙorafi.
 
Ya ce nan take su ka garzaya da shi asibiti.
 
Matashin, mai shekara 23, ya baiyana wa BBC cewa a dandalin sada zumunta na Facebook su ka haɗu da wanda ake zargi da yunƙurin halaka shi.
 
Ko a makon da ya gabata ma an kama wani matashi da ya yi wa wata yarinya ‘yar makotansu yankan rago a karamar hukumar Tofa a Kano, bayan ya nemi kudin fansa daga wajen iyayenta.