Gwamnonin Nijeriya na son Gwamnatin tarayya ta mayar da litar Man fetur 380

Gwamnonin Nijeriya na son Gwamnatin tarayya ta mayar da litar Man fetur 380

Gwamnonin Nijeriya na son Gwamnatin tarayya ta mayar da litar Man fetur 380

Bayan wata uku da gwamnatin Nijeriya ta fita batun kudirin kungiyar gwamnonin Nijeriya na son a mayar da litar man fetur daya naira 380, a jiya Jumu'a an sake gabatar da kudirin in da gwamnatin tarayya ta ce ba za ta aminta ba sai an cimma matsayar hakan da kungiyoyin ma'aikatan Nijeriya.
Da farko gwamnatin tarayya ta jingine bukatar gwamnonin Nijeriya na a janye tallafin Man fetur sai a rika sayar da litar Man 380 zuwa 408.5 tun a 21 ga watan Mayu, sai kuma ga lamarin ya sake dawowa.

Gwamnonin sun bayar da shawarar ne saboda kwamitin da Gwamnan Kaduna ya jagoranta ya ba da shawarar a bar kasuwar Man fetur ta ci gashin kanta, domin tallafin ba zai daure ba kuma masu sumogal da haramtaccin kasuwancin Man a makwabtan Nijeriya suke cin gajiyar tallafin.
Karamin ministan Man fetur Timipre Sylver ya ce har yanzu farashin yana nan kan 162 zuwa 165.
Ya ce farashin zai cigaba da kasancewa haka nan, har sai sun kammala yarjejeniya da kungiyoyin kwadago.
Ya ce ya zama wajibi su sanarwa mutanen kasa duk da nauyin da ke saman gwamnati ba ta gaggawar kara farashin man fetur.
Shugaban kungiyar masu sayarda man fetur a Nijeriya Dakta  Billy Gillis-Harry ya ce su 'yan kasuwar Man fetur na goyon bayan a cire tallafin man fetur.

Ya ce barin kasuwa ta yi hukuncin farashin man shi zai kawo samuwarsa yanda zai wadata.