Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'addar Boko Haram Da Dama A Borno

Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'addar Boko Haram Da Dama A Borno
 
 
 

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na bataliya ta 115 sun kashe ‘yan ta’addar kungiyar ISWAP/BokoHaram da dama a wani samame da suka kai a kauyukan Lassa da Kelle a jihar Borno.

 
A cewar wata ‘yar takaitacciyar sanarwa a ranar Juma’a, rundunar ta ce arangamar ta faru ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni, 2022.
 
Sojojin sun kuma kwato motar bindigu guda daya, motocin kirar Hilux guda biyu, makamai da alburusai.
 
Wannan shi ne na baya bayan nan a jerin nasarorin da sojojin Najeriya suka samu a cikin mako guda.
 
Tun da farko dai, jiga-jigan Sojoji na 29 Brigade sun kashe ‘yan ta’addar BHT/ISWAP da dama da suka tare hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a Goni Masari.
 
Bayan hare-hare masu zafi daga rundunar sojojin saman Najeriya an kashe da dama daga cikin 'yan ta'addan wasu da dama kuma suka tsere dauke da raunuka. 
 
An kwato makamai da alburusai da suka hada da magunguna iri-iri da na'urori masu kara kuzari, an kuma ceto mutane 5 da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su