Koyar da matasa sana'oi  ita kadai ce hanyar fita daga matsalar tsaro a Nigeriya-- Engr. Mustapha Ringim

Koyar da matasa sana'oi  ita kadai ce hanyar fita daga matsalar tsaro a Nigeriya-- Engr. Mustapha Ringim
 
 

Engr. Mustapha Habu Ringim wani kwararre Injiniya ne da ya yi fice a Kano da ma Nigeriya wajen horar da matasa Kimiyya da Fasaha da harshen Hausa, ko a kwanann nan kungiyar Alummar Hausawan duniya sun ba shi kanbin girmawa na sarautar Sarkin Fasahar Hausawan Afirka a tattaunawasa  da Ibrahim Hamisu a Kano za ku yi irin yadda ya horar da matasa cikin kankalin lokaci inda suka za ma masu dogaro da kansu ga yadda tattaunawar ta kasance:

 
Daga Ibrahim Hamisu
 
Za mu so ka gabatar mana da kanka?
 
Suna na Eng. Mustapha Habu Ringim, ni ne shugaban Kamfanin Engausa grobal Tech Of da Kuma chosen one Technology Limeted, ni ne ( sarikin Fasahar Hausawan Afirka), na yi Primary a Katutu Special Primary Ringim, na yi  science secondary a Kafin Hausa ta jihar Jigawa, tun a aji daya na babbar sakandire Ina cikin dalibai na farko-farko da suke zuwa na daya a bangaren computer. Nayi Diploma a School of Technology, da Kano state Polytechnic, na yi Digiri a Jami'ar Bayero Kano inda na karanci Electrical Engineering na kammala a shekarar 2010, kafin na kafa Kamfani na yi aiki da kamfanin ZINOX Computers wanda ya ke a Legas, kuma na yi aiki da kamfanin Telecom na ZTE wanda ya ke a Chaina wanda ya ke da reshe a Nigeriya amma ni a Chaina suka fara ba ni horo a jami'arsu da ke Chanzain, na yi aiki da su na shekara biyar.
 
Ta taya Kamfanin Engausa Global Tech Hub ya samo asali?
 
Da farko na bude Kamfanin Chosen one global Technology ne a Abuja daga nan sai na dawo da shi Kano, to a lokacin da na dawo na yi ta kokarin  jawo matasa masu Digiri, musamman wadanda suka karanci kimiyya da fasaha to sai na ga Mafi yawansu ba koyon Sanaa ne a ransu ba, sun fi tunanin su sami aiki a gwamnati ko wani babban Kamfani to sai naga bari in janyo wadanda suke ganin ba su da wani amfani a rayuwa ko suna ganin a karatun Boko ba su da wani amfani kuma Ba su da wata madafa a rayuwa, irinsu ne wadanda ance sun kasa cin Turanci da lissafi, to sai na ce bari in kira su na saukaka masu karatun Bokon, in saukaka masu kimiyya da Fasahar idan suka samu kwarewa in dauke su aiki su tsaya da kafarsu, wannan shi ne asalin kirkiro Ingausa, wannan dalilin ne ya sa aka sanya Mata suna Ingausa maana English/ Hausa, sai na zo na saukaka masu komai na rika koya masu da Hausa sai na ga sun ma fi wadancan da suka kammala digirin da na ke ta kwadayin sai na koyar da su kimiyya da fasaha da Turanci. Hakan ya sa na fahimci cewa akwai wasu matsaloli na alummarmu da wasu gurabe da shingaye da dama da ya kamata a Karya wadancan shingaye da suka hana matasanmu su yi amfani da kwakwalwar da Allah ya ba su su yi kerekere ko su yi sana'oi na zamani da za su samawa da kansu aiki, su daina shaye-shaye da zaman banza.
 
Yaushe aka bude Engausa?
 
An bude Engausa a shekarar 2019, a lokacin da aka bude ta kyauta ake yin karatu, Amma a 2020 aka yi masa rigista ya zama Kamfani, to a lokacin ne aka fara tallarta shi, mutane suka shigo har suka fara koyon sana'oin da suke tsayawa da kafarsu, Kuma har ma gwamnati ta ga abinda muke yi ta ba mu tallafi.
 
Daga lokacin da ka bude Kamfanin zuwa yanzu dalibai nawa ka yaye?
 
Daga lokacin da muka bude Kamfanin Engausa a shekarar 2020 zuwa yanzu mun yaye dalibai sama da 2000, Amma ita  chosen one Global kuwa, wanda Ita ce tushe, ba zan iya kididdige maka mutanen da muka ya ye ba, tun a 2015 Muka bude shi, mun yaye yan Polytechnic da yan Jami'a da dama. Saboda mun fara kirga wadanda muka yaye ne tun lokacin da aka fara biya.
 
Daga lojacin da fara zuwa yanzu wadanne irin nasarori za a iya cewa an samu?
 
Alhamdulillahi babbar nasarar da na samu ita ce na samun damar  canja al'ummata na cewa karatun Kimiyya da fasaha zaa iya yin shi da harshen uwa, laala bayan mutum ya koyi ilimin da harshen uwa, ya iya zuwa ya koya da harshen turanci, Larabci, Faranci ko kowane harshe ne da ya ke ganin zai taimaka masa ko zai ingiza karatun nasa ya zama yana alaka da sauran mutanen duniya, wannan kuma wani abu ne mai zaman kanta, amma dai shi yaren uwa ba ci baya ba ne, kamar yadda wasu suke zato ace wai Hausa kawai ka iya ba za ka iya komai ba, wannan ne ya sa mu muke dauko har almajirai da ba su taba zuwa makarantar Boko ba, ko wadanda sunje karatun Bokon amma ba su ci Turanci ba ballantana su tsallake su shiga makarantun gaba da sakandire ba, muka koyar da su wannan sannaoin na Zamani, wanda yanzu haka a cikinsu akwai malaman da suke koyarwa, wanda da sun kasa shiga makarantar Sakandire, Amma mu yanzu a nan Engausa Malamai ne kuma sun zama Malaman har wadanda suka ka karanci Degree na daya da na biyu har da na uku, akwai wadanda laccarori ne ma suna zuwa suna koyon sannaa ta zamani. Haka kuma samu karramawa sama da 20 kuma daya daga cikin manyan karramawar da akai min kwanan nan kungiyar alummar Hausawan duniya sun bani kanbi na sarautar Sarkin Fasahar Hausawan Afirka da kuma Lamar yabo ta ambasada na zaman lafiya, wanda aka na da min rawani a masarautar Dutse a taron Hausa na duniya, tabbas na ji Dadi da wannan karrama ni da suka yi, Alhamdulillahi.
 
Wadanne irin kalube ka samu wajen Gina wadannan Kamfanoni na ka da har ya kai wannan cigaba?
 
Kalubalen shi ne irin yadda na dinga samun kalubalen daga wajen masu ilimi wato Yan Boko da jami'o'i, domin sun za ta na kirkiro Engausa ne don na yi yaki da karatun Jami'a ne, saboda sun sha ji Ina fada cewa na fi jin dadin zama da wadanda ba su yi degree ba, manyan  lakcarori da farfesoshi sun sha kalubalanta ta cewa ba za a iya yin karatun kimiyya da fasaha da harshen uwa ba, Amma da yawa daga cikinsu bayan na shekara 3 zuwa 5 da fara Engausa sai gashi sun fahimci me nake nufi.
Mu anan Engausa kashi 90 a aikace mu ke yi, kashi 10 shi ne karatu wato (Theory). Don haka yanzu mun samu fahimtar juna, kalubalen ya zama alheri yanzu jami'oin za ka ga sun kawo mana ziyara suna so mu je mu dauki Engausa mu je mu bude Mata wani reshe a cikin jami'oin, ta yadda za ka ga yaran sun fita da riba biyu ga kwalin digiri ga na koyon sana'a.
 
Sai kalubalen na gurin zama, wannan gurin  Gwamnati ce ta ba mu aro a nan Farm center,  shekaru 2 ko 3, Kuma yanzu mun cinye kusan shekara biyu yanzu, don haka kalubalenmu yanzu mu sami babban gurin zama, wanda idan Allah ya ba mu za mu ninninka matasan da muke fitarwa.
 
Mene ne kiranka na karshe ga al'umma da  kuma ita kanta gwamnati?
 
Kirana ga al'umma su kara lura da tasirin da Engausa ta samu a cikin shekara 2 zuwa 3 saboda mun fassara kimiyya da fasaha zuwa harshen uwa. Kuma ya kamata a sani cewa duk wani matashi da aka gani a unguwa da baya jin turanci in dai ya na da basira da fasaha ko wata baiwa da aka gano to kar a barshi sakaka ba tare da wanda zai lura da shi ba, irin wadannan matasan arziki ne a raine su har su samar da aiki ga sauran matasa. Don haka nake jan hankalin al'umma da su gane cewa hanyar koyar da matasa sana'oi ita ce hanya daya tilo ta fita daga wannan masifa ta rashin zaman lafiyar da kuma katutun talauci. gwamnati kuwa su maida hankali wajen karfafa gwiwar irin wadannan cibiyoyi na mu, da ma na gwamnati,  da yawa sun mutu, an kirkiro su an zuba masu kaya amma an brufe su. wanda hanya ce da zaa samar da mafita a cikin al'umma, kuma Ina kira ga gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu, da su kara mana gwarin gwiwa wajen daukar nauyin matasa na unguwanni marasa aikin yi da yan baiwa.