Dalibban Kwaleji Sun Kashe wadda Ta Zagi Manzon Allah, 'Yan Sanda Sun Kama Dalibi Biyu

Dalibban Kwaleji Sun Kashe wadda Ta Zagi Manzon Allah, 'Yan Sanda Sun Kama Dalibi Biyu

 

 

Dalibbai a kwalejin ilmi ta Shehu Shagari dake Sakkwato  Sun kashe abokiyar karatunsu bayan ta zagi Manzon Allah a kafar sadarwar zamani ta wasup.

Dalibar mai suna Daborah Samuel  ta yi zagin ne kan hasalata da 'yan uwanta suka yi na tura abubuwan da suka shafi manzon Allah a group na karatunsu wanda take ganin hakan bai dace ba.
Matasan sun fusata suka nemo ta a cikin makaranta suka kashe ta anan take suka kona gawarta.
Bayan nan hukumar makaranta ta bayar da sanarwa rufe kwalejin sai yanda hali ya yi, da umarta dalibai su bar makarantar nan take, gwamnatin jiha ta aminta da hakan ta kuma kara tabbatar da matakin.
Jami'in hulda jama'a na 'yan sanda Sanusi Abubakar ya ce rundunar 'yan sandan jihar sun fara bincike kan lamarin kuma sun kama dalibi biyu kan zargin suna da hannu a kan daukar doka a hannu.