Maganin matsalolin da ake fuskanta a kasar nan------Sarkin Musulm

"Kawo mu da ya yi a Nijeriyar nan wuri daya ba kuskure ba ne haka yake so, in har yana son wani abu daban zai yi abinsa ba tare da kowa ya sani ba, dole mu karbi abin da addininmu ya aminta da shi a matsayinmu na kiristoci da musulmai masu biyayya. 

Maganin matsalolin da ake fuskanta a kasar nan------Sarkin Musulm
Maganin matsalolin da ake fuskanta a kasar nan------Sarkin Musulmi

Maganin matsalolin da ake fuskanta a kasar nan------Sarkin Musulmi

Yakamata a kawar da kabilanci a zama 'yan uwan juna 

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya yi kira ga dukkan kabilun Nijeriya su riki juna a matsayin 'yan uwa domin Allah da ya halicci kabilun daban-daban ba ya kuskure.

A lokacin da ya yi jawabi a wurin bukin karrama shugabanni a Abuja ranar Alhamis Sarkin Musulmi ya nuna cewa kowa ya dauki na shi ne mutum ba za a yi maganin matsalolin da ake fuskanta a kowace kabila ba, amma in aka zo aka hadu wuri daya za a samu maslahar warware su.

Rayuwar mata bayan sun rasa mazajensu.....

Ya ce in har aka rika tafiya da dimbin hanyoyin da ake da su, ta ina za a samu daidai, Allah ba ya taba kuskure, haka yake dole ne a yi biyayya da hakan.

"Kawo mu da ya yi a Nijeriyar nan wuri daya ba kuskure ba ne haka yake so, in har yana son wani abu daban zai yi abinsa ba tare da kowa ya sani ba, dole mu karbi abin da addininmu ya aminta da shi a matsayinmu na kiristoci da musulmai masu biyayya. 

"Dukkanmu mun sani da tsatso daya aka halicce mu." in ji Sarkin Musulmi.

Katsina tabi sahun Zamfara an rufe layin waya