‘Yan Sanda Sun Kuɓutar Da ‘Yan Makarantar Islamiyya Su 21 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu yara 'yan makarantar Islamiyya, da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, su 21 a kauyen Kucheri da ke karkashin karamar hukumar mulkin Tsafe tare da malaminsu da direban Bas da zai kai su makaranta.
Da yake gabatar da yaran a hedikwatar ‘yan sanda a Gusau a yau (Asabar), kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ayuba Elkana, ya ce a lokacin da suka karbi kiran gaggawa, rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji sun mayar da martani tare da kama ‘yan bindigar da wata babbar bindigar yaƙi.
“A ranar 31 ga Disamba, 2021, an samu kiran mun samu kiran gaggawa daga Kauyen Kucheri ta hanyar karamar hukumar Tsafe cewa, ‘yan bindiga da dama sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtua da ke Kucheri, suka kuma yi awon gaba da wasu matafiya dake cikin motoci har guda 5 daban-daban.
Jami’an tsaro na ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji sun yi gaggawar amsa kiran da aka yi musu suka isa wurin, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.
“Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar ceto yara 21 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata biyu (2) da suka fito daga kauyen Rini da ke karamar hukumar mulkin Bakura, kuma Almajirai tare da Malaminsu mai suna Lawali Ibrahim, da kuma direban motar su kirar Hummer. daga cikin wadanda abin ya shafa da ake garkuwa da su a halin yanzu,” in ji Kwamishinan.
CP Elkana ya kuma yi kira ga jama’a musamman direbobi da fasinjoji da su daina tafiye-tafiyen dare, yana mai jaddada cewa, lokacin dare shi ne lokacin da ‘yan fashin ke amfani da su wajen toshe hanya da kuma yin garkuwa da matafiya a jihar.
Ya ba da tabbacin tabbatar da aikin sintiri na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, musamman a duk hanyoyin da suka hada jihar da sauran jihohi makwabta.
managarciya