Ayyukan dogaro da kai: Gwamna Buni ya raba motoci 100 bashi ga direbobi a jihar Yobe

Ayyukan dogaro da kai: Gwamna Buni ya raba motoci 100 bashi ga direbobi a jihar Yobe

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

A kokarinsa na farfado da harkokin tattalin arziki, ayyukan yi da dogaro da kai a jihar Yobe, Gwamnan jihar, Hon. Mai Mala Buni ya kaddamar da raba motoci 100 bashi ga direbobi, tallafin kudi ga yan kasuwa da masu kananan sana'o'in hannu, zawarawa da maras galihu a jihar Yobe.

Da yake kaddamar da raba kayan, da yammacin ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar dake Damaturu, Gwamna Buni ya ce gwamnatin jihar ta kashe naira mikiyan 461,125,000 wajen sayo motoci kirar Toyota (Avensis) 100, domin raba su bashi ga direbobi 100 a jihar kan farashin naira miliyan 2 (N2m); kowace mota daya, kuma za a biya cikin shekaru biyu.

Sauran kayan tallafin sun hada da kekunan dinki, injinan markade, da makamantan su, wadanda aka raba ga daruruwan jama'a. Da tallafin jari ga zawarawa 400, maras galihu 254 tare da masu sana'o'in hannu, manya da kanana kimanin 1600. Har wala yau da ware naira biliyan 1,356,000,000 domin tallafa wa kananan yan kasuwa. 

A hannu guda kuma, Gwamna Buni ya ce, "Na umurci ma'aikatar bunkasa tattalin arziki, walwala da samar da ayyukan yi, ta yi hadin gwiwa da Yobe Microfinance Bank kan tsare-tsaren da suka dace wajen biyan bashin wadanda suka ci gajiyar motocin." 

"Mun kirkiro wannan tsari ne wajen tallafi ga yan kasuwa, zawarawa, maras galihu don sake farfado da harkokin tattalin arziki, samar da ayyukan yi da dogaro da kai, domin al'umma su samu walwala da ingancin rayuwa."

"A shekaru uku da suka gabata, mun aiwatar da ayyuka da dama da suka kunshi bunkasa rayuwar al'umma tare da bayar da horo na musamman a karkashin shirin mu na sake farfadowa daga kalubalen da jiharmu ta fuskanta a baya na matsalolin tsaro, domin inganta rayuwar jama'a wajen samun abubuwan dogaro da kai da habaka harkokin ci gaban tattalin arziki ga al'ummar wannan jihar."

 "A wannan karon za mu sake kaddamar da wani tallafi na daban ga daidaikun jama'a da Kungiyoyin yan kasuwa, a matsayin samar da ayyukan yi, habaka harkokin tattalin arziki, don jama'a su samu abin dogaro da kai."

Gwamna Buni ya nanata cewa, "Dukan wannan matakan su na gudana ne a karƙashin shirin bayar da tallafi na musamman ga masu karamin karfi da kananan yan kasuwa, domin sake farfado da al'ummar da matsalar tsaro ta shafa a wannan jihar tamu; a shekarun baya."