Hukumar EFCC  Ta Gurfanar Matashi A Kotu Kan  Zambar Miliyan 15

Hukumar EFCC  Ta Gurfanar Matashi A Kotu Kan  Zambar Miliyan 15

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Wani Mutum Zai Yi Zaman Gidan  Yari Na  Shekara Daya Saboda Zambar N15.4 A Maiduguri 

A ranar litinin, 31 ga watan Janairu, 2022, mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Barno ta yanke ma wani mai suna Bashir Mohammed Karube hukuncin zaman gidan yari na shekara daya bayan hukumar EFCC ta gurfanar da shi inda take tuhumar shi da laifin cin amana ta kudi kimanin Naira miliyan goma sha biyar da dubu dari hudu.

Hukumar EFCC ta tuhume shi da karban kudin a hannun wani mai suna Mohammed Bukar Customs da niyyar siyo masa Keke Napep guda ashirin amma daga baya ya karkatar da kudin.

Wanda aka tuhuma ya musanta laifin dalilin da ya sa aka fara sauraren shari’a da gabatar da shaidu biyar da sauran hujjoji.

A lokacin yanke hukuncin, mai shari’a Kumaliya ta kama Karube da laifin sannan ta yanke masa hukuncin zama gidan yari na  shekara daya ko biyan tara da Naira dubu hamsin.

Sannan mai shari’a ta umarcee shi da ya mayarwa wanda ya zambata kudinshi Naira miliyan goma sha biyar ko kuma ya yi zaman shekaaru goma a gidan yari.

Ku ziyarci sashen intanet na EFCC a www.efccnigeria.org don Karin bayani da karanta sauran labaran EFCC.