Ta nemi mijinta ya sake ta domin yana lakaɗa mata duka don bata ƙoshi

Wata matar aure mai shekara 23 ta nemi kotun shari'ar musulunci dake Kaduna ta raba aurenta da mijinta saboda dukanta da yake yi don ya ce bata ƙoshi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato matar mai suna Firdausi tana shaida wa kotun cewa mijin nata, Haruna, kan kulle dakin girki idan dare ya yi.

“Mahaifina ne ya tilasta ni auren Haruna ina da shekara 16, kuma a shekara bakwai din da muka yi tare, ba a taba shekara guda cur bai kora ni gida ba.

“Bayan haka, ya hana kowa zuwa wurina da abin ya ishe ni, iyayena kuma suka ji labarin abin da ke faruwa, suka kai kara wajen mahaifiyarshi, sai ta ce wai ya yi gamo ne”, inji Firdausi.

Lauyan Haruna, M.K. Mustapha, ya ce “Wanda nake karewa bai yi kama da mai tabin hankali ba. Hasali ma, yanzu haka yana Katsina yana wani aiki.”

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, ya umarci lauyan Haruna ya gayyato iyayen ma’auratan saboda a warware matsalar cikin ruwan sanyi, sannan ya dage sauraren kara zuwa 4 ga watan Oktoba.

Matar bata nuna ba ta ƙoshi ba kamar yadda mijin nata yake zargi a ƙararsa da ta kawo.