Bazan Yi Ƙasa a Guiwa Ba Har Sai Na Ƙwatowa Al'umma Haƙƙinsu----Barista Sada'atu Yunusa

 Bazan Yi Ƙasa a Guiwa Ba Har Sai Na Ƙwatowa Al'umma Haƙƙinsu----Barista Sada'atu Yunusa

 
 
Barista Sa'adatu Yanusa Muhammad mace tilo dake takarar kujerar majalisar tarayya a Sakkwato, sai dai jagororin jam'iyarsu ta APC a Sakkwato sun shirya wata munakisa naganin bata samu nasara ba duk da dimbin magoya baya da take da su a yankinta na kananan hukumomin Bodinga da Dange Shuni da Tureta.
Barista a zantawarta da manema labarai ta fadi matsayarta kan zaben fitar da gwani da aka ce an gudanar a karamar hukumar Bodinga.
"bayanai sun watsu ko'ina a kafafen yada labarai zaben fitar da gwani da aka yi na cike da rashin gaskiya da sabawa ka'idar zabe tun matakin farko da aka sauya ranar gudanar da shi daga Jumu'a zuwa Assabar ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba misalin 'yan takara, aka sauya sunayen daliget da wasu daban lokaci kadan kamin soma zabe, jami'an tsaron 'yan sanda suka rika musgunawa mutane abin da ya kai ga rasa ran wasu da ba su ji ba su gani ba, kawai saboda wasu manya na bukatar daura yaronsu a takarar bayan kuma al'umma sun nuna ba su bukatarsa,". a cewarta  
Ta yi kira ga magoya bayanta su cigaba da zaman lafiya musamman halin da ƙasar take ciki.
"yakamata su sani muna kan ƙoƙarinmu mu tabbatar mun dawowa jama'a abin da suka yi yaƙini kansa bisa ga abin da aka yi a zaɓen da ya gabata na ƙwace hakkinsu.
"a matsayina na mai biyayya ga jam'iyarmu ta APC ina kyautata zaton jam'iyarmu za ta duba lamarin domin tafiya ce ta adalci a tafiyar dimukuraɗiyya ana wanzar da adalci ne a tsakanin al'umma.