Zabar Mataimaki: Sanata Wamakko Na Cikin Mutanen Da Kwamitin APC Ya So Tinubu Ya Zaba

Zabar Mataimaki: Sanata Wamakko Na Cikin Mutanen Da Kwamitin APC Ya So Tinubu Ya Zaba

Bayan dan takarar shugaban kasa a jam'iyar APC Bola Tinubu ya samu nasarar tsayawa takarar shuaban kasa, sai aka fara neman wanda zai  mara masa baya a matsayin mataimakinsa.

Tinubu da kansa ya ce yana tattaunawa da mutane sosai kan wanda zai zaba a matsayin mataimakinsa, yana jindadin yanda lamurra ke tafiya a tsakanin jagororin jam'iya da makusantansa da masu ruwa da tsaki na kasa.

Majiya mai tushe a jam'iyar APC ta sanar da Daily Trust akwai kwamitin APC  wanda tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya jagoranta sun jinjina mutane sun fitar da mutum 11 da ya kamata Tinubu ya zabi daya daga cikinsu.

Mutanen da ake ganin yakamata Tinubun ya zabi daya daga cikin su kafin ya yi gaban kansa ya dauko wanda kwamitin bai shigo da shi ba, sun hada tsohon kakakin shugaban majalisar wakillan Nijeriya Yakubu Dogara da mataimakiyar sakataren  majalisar dunkin duniya Amina J. Mohammed da Kashim Imam daya daga cikin makusantan Tinubu, sai Ambasada Fatima Balla da Sanata  Anthony Manzo.

A arewa ta yamma kwamitin ya mika sunan  Hajiya Najatu Mohammed, El-Rufai, da tsohon gwamnan Sakkwato  Sanata  Aliyu Magatakarda Wamakko, da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu.

Kwamitin ya aminta da Gwamnan Borno Babagana Zulum da a bashi matsayin na dan takarar matimakin shugaban kasa.

Bayan kwamitin ya mika rahoton ga Tinubu sai kawai aka ji ya ayyana suna tsohon gwamnan Borno Kashim Shattima matsayin wanda zai mara masa baya duk da baya cikin 11 da aka bayar da shawara kansu.