Matukar uwar jam'iyar APC ba ta yi mana adalci ba za mu dauki mataki na gaba-----Honarabul Salame

Honarabul Salame wanda ya yi zabensa daban tare da magoya bayansa, a gefe daya kuma shugabannin jam'iya a jihar Sakkwato  tare da wakillan uwar jam'iya da hukumar zabe sun aiwatar da nasu daban.

Dan majalisar wakillai dake wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela Honarabul Abdullahi Balarabe Salame ya bayyana matsayarsa a zaben kananan hukumomi da jam'iyarsa ta APC ta gudanar a ranar assabar data gabata in da ya koka kan yadda zaben ya gudana, kuma za su nemi hakkinsu yanda dokar jam'iya ya tanadar don neman a yi masu adalci.

.
Honarabul Salame wanda ya yi zabensa daban tare da magoya bayansa, a gefe daya kuma shugabannin jam'iya a jihar Sakkwato  tare da wakillan uwar jam'iya da hukumar zabe sun aiwatar da nasu daban.
Salame ya ce "yakamata ace in wane da wane da za su yi takara masu ruwa da tsaki su sulhunta su, shi ne ake kira an yi sulhu amma ba su saurare mu ba,  mun ce kowane gari su fitar da wanda suke so mu ba mu da dan takara sai wanda mutane ke so ne za a zaba.
"Za mu rubuta korafi mu kai ga uwar jam'iya ya rage ga uwar jam'iya ta bincika ta yi adalci ga abin da ta binciko, in ba ta yi adalci ba, za mu zauna mu ga abin da yakamata wanda ba a yi wa adalci ba, ya yi sai mu dauki matakin da yakamata." a cewar Salame.
Wani jigo a APC ya ce duk wadan da suka shirya zabe da kansu wannan shirme ne suka yi domin sun yi gaban kansu, ba da izinin jam'iya da hukumar zabe ba.
Ya ce ba wani sakamakon zabe da za a amince da shi bayan  zaben da wakillan jam'iya suka gudanar.