Tambuwal Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Tsinci Kansu Cikin Tsadar Rayuwa

Tambuwal Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Tsinci Kansu Cikin Tsadar Rayuwa

 

Tsohon gwamnan jihar Sokoto,  Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya ɗora alhakin halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki kan sake zaɓen jam'iyyar APC da suka yi a zaɓen 2023. Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu, ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun yi babban kuskure sake dawo da APC kan karagar mulki. 

Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Sokoto ranar Lahadi, 2 ga watan Yunin 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sun gargaɗi ƴan Najeriya kan sake zaɓen jam'iyyar APC amma suka yi kunnen uwar shegu da jan kunnen da aka yi musu. 
"A lokacin yaƙin neman zaɓe a 2023, mun gargadi ƴan Najeriya da kada su sake yin kuskuren zaɓen APC a mulki domin ba su da wani abin kirki da za su iya yi." 
"Mun ce musu APC ba ta shirya shugabancin ƙasar nan ba. Abin da suke so shi ne su ƙwace mulki su gan su a cikin ofisoshi." 
Sai dai tsohon gwamnan ya yi kira ga ƴan adawa da su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta sha kaye a zaɓe mai zuwa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar. "Haƙƙi ne a kanmu mu haɗa kai domin tabbatar da cewa APC ta yi rashin nasara a a dukkanin matakan gwamnati." - Tambuwal Ya yabawa shugabannin jam’iyyar bisa yadda suka haɗa kan jam’iyyar wanda hakan ya sanya ƙarfinta ya ƙaru.