Jam'iyyar ADC ta buƙaci mambobin ta su daina raba ƙafa su kuma yi murabus na din-din-din daga sauran jam'iyyu 

Jam'iyyar ADC ta buƙaci mambobin ta su daina raba ƙafa su kuma yi murabus na din-din-din daga sauran jam'iyyu 

Jam’iyyar ADC ta buƙaci mambobinta su daina raba ƙafa, su yi murabus daga sauran jam’iyyu sannan su mai da kai da ccikakken alƙawari ga ADC.

BBC ta rawaito cewa wannan na daga cikin manyan matakai uku da aka cimma a taron sirri da mambobin jam'iyyar suka gudanar a Abuja ranar Alhamis, wanda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya halarta tare da manyan shugabannin jam’iyyar.

A cikin taron, wanda shugaban jam’iyyar na ƙasa, David Mark, ya jagoranta, an tattauna hanyoyin haɗin kai da dabarun da za a yi amfani da su domin tunkarar zaɓen 2027.

Haka kuma, dukkan masu sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa sun amince cewa za su goyi bayan wanda ya fito daga cikin su bayan an kammala zaɓen fidda gwani.

Atiku Abubakar ya tabbatar da halartar taron ta shafin sa na X, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkuri na haɗin kan ’yan adawa.

Daga cikin mahalarta akwai tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal da dai sauransu..

Sai dai ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, bai halarci taron ba, amma ya aike da sakon cewa yana tare da su.