2023: Gidauniyar Sa'ar Mata Ta Kaddamar Da Kayan Kamfe  Ga Jam'iyar APC A Sakkwato

2023: Gidauniyar Sa'ar Mata Ta Kaddamar Da Kayan Kamfe  Ga Jam'iyar APC A Sakkwato

 

 

Gidauniyar Sa'ar Mata ta kaddamar da kayan kamfe da suka kunshi Turame na alfarma dake dauke da hutanan dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dana Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto, kayan sun hada da hula P-Caps da Gyale da hijabi da  sauransu.

An Kaddamar da kayan a babban dakin taro na Otal din Soul Care a jihar Sakkwato domin kara zaburar da magoya bayan jam'iyar APC a yunkurin Gidauniyar ga samar da nasara.

Matar Dan takarar Gwamna Hajiya Fatima Ahmad Aliyu a wurin taron ta ce an fito da hakan ne don a zaburar da mata da matasa a samu goyan bayan da jam'iyar za ta yi nasara a jiha da kasa baki daya.

Hajiya Fatima ta ce mata sun fito yi wa dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa da Gwamna da mataimakinsa kuri’a don  tabbatar da sun samu nasara a 2023.

 Ta ce lokaci ya yi da mata za su fito domin nemawa kansu mafita ga mutanen da ba su san darajarsu ba.

"abubuwan da ke kasa a yanzu da irin sauya sheka da ake yi ana shigowa jam'iyarmu ya nuna APC ce za ta samu nasara a zabe mai zuwa."

Wadda ta shirya bukin shugabar Gidauniyar  Barista Sa'adatu Yanusa Muhammad ta ce abin da ake son a cimma ga irin wannan hobbasar shi ne shigar mata a dama da su a siyasa ba Sakkwato kawai da Arewacin Nijeriya a cikin jam'iyar APC dake gaba a jiha da kasa baki daya, a ko’ina.

Barista Sa'adatu ta ce Gidauniyar ta fito da hanyar yekuwar bin gida-gida don jawo hankalin mata ga zabar jam'iyar APC wani abu ne da zai taimakwa jam'iyar ga samun nasararta a babban zabe dake tafe.

"mun yi wannan hobbasar ne domin shigo da mata a cikin siyasa su bar barin ana barinsu a baya, don siyasa  mata nada rawar da za su taka sosai a samar da al'umma ta gari.

"APC nada damar da za su yi nasara a Nijeriya baki daya, jam'iyarmu nada magoya baya sosai abin da kawai ke gabanmu mu samar da hanyoyi da za mu tsare kuri'unmu a tabbatar an sanar da wanda mutane suka zaba." a cewarta. 

Barista wadda ta fito karo biyu tana neman a tsayar da ita, takarar 'yar majalisar tarayya da zata wakilci kananan hukumomin Bodinga da Dange Shuni da Tureta har yanzu hakarta bata cimma ruwa ba, ta ce abin da ya sa har yanzu ba ta gaji ba, take harkokin jama'a domin siyasa a cikin jininta take ta fara tun tana makaranta, ta san wani lokaci za ta yi nasara don haka ne ba ta karaya ba don yiwa jama'a hidima shi ne gabanta.