Rikicin PDP: Kwamitin Amintattau Ya Nemi Tambuwal Ya Gaggauta Kiran Taron Gwamnonin Jam'iya

Rikicin PDP: Kwamitin Amintattau Ya Nemi Tambuwal Ya Gaggauta Kiran Taron Gwamnonin Jam'iya

Tambuwal Zai Samu Nasarar Tara Gwamnonin PDP a wannan marar da ake ciki?

 
Kwamitin amintattun jam'iyar PDP a zaman da ya yi Jumu'a data gabata ya cimma wasu matsaya kan rikicin da ya dabaibayi jam'iyar ya hana mata sakat da rawar gaban hantsi.

Shugaban kwamitin Sanata Adolphus Wabara a takardar bayani da ya sanyawa hannu ya ce shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya kira taron mambobinsa ba tare da wani bata lokaci ba.
Haka ma BOT sun yi kra ga mambobsinsu su saisaita harshensu a wurin gabatar da jawabai da tattaunawa a gaban jama'a.
Ya ce duk matsayar da suka cimma za su gabatar da ita a gaban majalisar zartawar jam'iya.

A cikin abin da suka amince har da kin aminta da shugaban jam'iya Ayu ya yi murabus abinda shi ne ke kara rura wutar rashin fahimta a tsakanin tsagin Wike da Atiku.