An Shawarci 'Yan Jam'iyyar APC A Zamfara Da Su Guji Siyasar Ta Ɓare Kowa Ya Rasa Da Sanata Kabiru Marafa Ke Yi

Yace, Kabiru Marafa ya fito ne domin ya kawo rudani cikin jam'iyyar da a ka sani a matsayin tsintsiya madaurin ki daya. "Ina mai sheda maku cewa Kabiru Marafa ko takar dar zama dan jam'iyyar APC ba yada, saboda had yanzu bai sabunta takar dar saba lokacin da akayi rajistar yayan jam'iyyar APC na gaskiya. " Ina mamakin wanda ko rajistar zama dan jam'iyyar APC bai sabunta ba, wai ya koma gefe daya yace yayi zaben shugaban nin mazabu, kuma ba yada ko izinin yin hakan da hukumar zabe ta kasa watau (INEC) ta bashi"inji Shinkafi

An Shawarci 'Yan Jam'iyyar APC A Zamfara Da Su Guji Siyasar Ta Ɓare Kowa Ya Rasa Da Sanata Kabiru Marafa Ke Yi
Shinkafi

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Wani jigo a jam'iyyar APC a Zamfara, Dakta  Sani Abdullahi Shinkafi, yayi kira ga yayan jam'iyyar dake jiha Zamfara da su guji irin siyasar da  tsohon sanata Senator Kabir Marafa keyi na raba hankulan su, domin ta bare kowa ya rasa.

Wanban  Shinkafi ya yi wannan kira ne yau a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau babban birnin jihar, dan gane da kammala zaben shuga bannin jam'iyyar APC a matakin mazabu guda 147 dake fadin jihar.

Yace, Kabiru Marafa ya fito ne domin ya kawo rudani cikin jam'iyyar da a ka sani a matsayin tsintsiya madaurin ki daya.

"Ina mai sheda maku cewa Kabiru Marafa ko takar dar zama dan jam'iyyar APC ba yada, saboda had yanzu bai sabunta takar dar saba lokacin da akayi rajistar yayan jam'iyyar APC na gaskiya.

" Ina mamakin wanda ko rajistar zama dan jam'iyyar APC bai sabunta ba, wai ya koma gefe daya yace yayi zaben shugaban nin mazabu, kuma ba yada ko izinin yin hakan da hukumar zabe ta kasa watau (INEC) ta bashi"inji Shinkafi.

Ya kara da cewa, Kabiru Marafa yana son ya kawo rudani ne kawai ga jam'iyyar APC a Zamfara, tunda uwar jam'iyyar bata san kowa ba sai wayanda suka fito ta bangaren gwamna Muhammed Bello Matawalle.

Daga nan sai yayi kira ga Marafa da yaje ya sabunta rajistar sa ta zama dan jam'iyyar APC, sannan yazo yabi gwamna Bello Muhammed Matawalle, domin a kawo ci gaba ga jama'ar wananna jihar. Hasali ma wajen sha'anin tsaro da ya dabai baye jiha. 

 Ya shawarce shi da ya guji siyasan tar da sha'anin tsaro domin abune wanda ya shafi kowa da kowa.

 "Gwamna Bello Muhammed Matawalle shima ya gaji wannan matsalar ne, adon haka ya kamata kowa ya aje batun siyasa a taho ayi irin zaman da gwamnan Sakkwato yayi da duk wani mai fada a jiya, ba maganar siyasa, kuma duk irin su tsofafin gwamnoni kamar su Bafarawa, Aliyu Magatakar da Wamakko da dai sauran su sun halarci taron.

Daga karshe Wanban Shinkafi ya kara kira ga duk wanda bai sabunta rajistar saba musamman tsohon gwamna Alhaji Abdul Aziz Yari Abubakar da Magoya bayan sa da suyi hakan kafin damar da aka basu ta wuce.