Bana ƙyashin baiwa ƙananan hukumomi cin gashin kan su -- Buni 

Bana ƙyashin baiwa ƙananan hukumomi cin gashin kan su -- Buni 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce shi matsayar sa ita ce cewa ba ya nuna adawa da baiwa ƙananan hukumomi cin gashin kan su a Nijeriya.

Buni ya baiyana hakan ne bayan ya kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomi a rumfar zaɓe ta Buni Gari a ranar Asabar.

Ya ce aikin da gwamnatin sa ke yi da ƙananan hukumomi ya nuna yadda yanke basu damar gudanar da aiyukan su.

Gwamnan ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa nan gaba cin gashin kan ƙananan hukumomi zai dawo.