Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Shugaban ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato  Honarabul Isah Salihu Bashir Kalanjeni na jam'iyyar PDP mai mulki ya fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC mai adawa.
A  cikin daren Assabar ne  ɗaya daga cikin Chiyamomin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sanarda yanken hukuncin a lokacin da ya tafi gidan jagoran jam'iyar APC a Sakkwato Sanata Aliyu Mahatakarda Wamakko.
Shugaban ƙaramar hukumar bai sanar da dalilinsa na ficewa a jam'iyar ba, amma da yawan mutane na danganta hakan da hana masa tikitin takarar ɗan majalisar tarayya da zai waƙilci ƙananan hukumomin Tangaza da Gudu da Gwamna Tambuwal ya yi, duk ya sanar masa da cewa alƙawali ne yake son ya cika don haka ba zai ba shi damar ba, sai dai bai gamsu da hakan ba shi ne dalilinsa na barin tafiyar PDP.
Magoya bayan jam'iyar PDP sun nuna takaicinsu kan matakin da Kalenjeni ya ɗauka in da suke danganta lamarin da Butulci saboda amintakar da ke tsakaninsa da Tambuwal.