Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana goyon bayansa ga takarar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta shugaban kasa a shhekarar 2023.
Attahiru Bafarawa a wurin taron kaddamar da kungiyar cigaban yankin da samar da zaman lafiya Sakkwato ta Tagabas ne ya sanar da hakan a garin Gwadabawa a wannan Assabar, ya ce suna goyon bayan takakarar Gwamna Tambuwal ta shugaban kasa kan haka wannan yanki na su ya goyi bayan takarar ta Tambuwal.
Bafarawa ya ce yankin su ne na farko da suka nuna amincewarsu ga takarar ta Tambuwal, in da suka riga sauran yankuna biyu dake jihar Sakkwato.
"In Allah ya ba shi ya ba mu, mai girma gwamna wannan yanki namu sun fara bayyana amincewarsu ga takararka na cewa kai ne dan takarar shugaban kasar mu, mun riga sauran yanki ga bayyana wannan amincewar," a cewar Bafarawa.