Ayyuka Da Halin Tambuwal Nakawaici A Siyasa Suka Sa Na Dawo PDP------ Abdullahi Hassan

Ayyuka Da Halin Tambuwal Nakawaici A Siyasa Suka Sa Na Dawo PDP------ Abdullahi Hassan

 

 

 

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sakkwato ta Arewa Abdullahi Hassan ya bayyana dalilinsa na sake komawa tsohuwar jam'iyarsa ta PDP domin ba da tasa gudunmuwa a kafa gwamnati a 2023.

Abdullahi Hassan wanda aka fi sani da Mai malale ya ce ya koma PDP ne domin aiyukkan da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya shimfiɗa musamman a wa'adin mulkinsa na biyu abin sai sambarka gaskiya, ga shi da halin kawaici a siyasa baya riƙe abokin adawa da gaba shi yana siyasa ba da gaba ba.

"Ka dubi gadar sama guda biyu da ya shimfiɗa a Sakkwato ɗaya a Unguwar Rijiyar Ɗorawa, ɗayan a Runjin Sambo, ya samar da katafariyar asibiti ta zamani mai ɗaukar gadaje 1000, ga Sikandaren mata zalla ta kimiya duk a Ƙasarawa, ya samar da filin wasa na zamani a wurin da yake ƙoƙarin gina sabuwar Sakkwato.

"Tambuwal ya magance matsalar ambaliyar ruwa a unguwar Mabera, ya gina tagwayen hanyoyi a Waziri Abbas dake uguwar rogo da Kan titin Sarkin Musulmi Dasuki da Mai Tuta, da Runjin Sambo da   sauransu.

"Ya gina gidajen ruwa na murtsatse a ƙananan hukumomin Sakkwato don kawar da matsalar ruwa a karkara, ya tallafawa ƙananan 'yan kasuwa da tallafin jari a bankin  kasuwaci na Giginya da gwamnatinsa ta samar, abubuwan da yawa", a cewar Mai Malale.

Abdullahi ya ce  yanzu ya dawo gida(PDP) domin a jam'iyar ne ya yi mulkinsa na shugaban ƙaramar hukuma.

Ya ce Tambuwal ɗan siyasa ne na gari yana barin kowa ya faɗi ra'ayinsa ba tare da tsangwama ba ko ƙoƙarin kawo cikas ga ɗan adawa, 'halin ta Tambuwal na kawaici da tafiyar da siyasa ba da gaba ba abin so ne a tafiyar siyasa hakan ne ke sa yana samun nasara kan 'yan adawarsa.

 

'Hangen nesansa  ne ya sa ya zaɓo Malam Ubandoma domin ya gaje shi, saboda  zaman amanar da ke tsakaninsu ya tabbata halin Malam na cigaba ne da ƙoƙarin kwatanta gaskiya, in Sakkwatawa suka dace da wannan zaɓi ya jagorance su za su samu cigaba ƙwaran da gaske, cikin mutinci da mutuntawa,' a cewar Abdullahi Hassan.