2023: Dubban ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Sokoto

2023: Dubban ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Sokoto


Dan takarar gwamna na jam’iyyar  PDP a jihar Sokoto, Mallam Saidu Umar, ya karbi mambobin jam’iyyar APC  2,343 zuwa cikinsu. 

Dubban magoya bayan na APC sun sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar ne a yankin Mainiyo da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.
Umar ya karbi sabbin ‘ya’yan PDPn ne a wani taron kaddamar da kungiyar ci gaban tsohuwar kasuwa ta Ubandoma/Sagir dake Mainiyo da kuma kaddamar da shirin bayar da tallafi da kungiyar ta kafa a yankin karkashin shugabancin shahararren dan kasuwa, Alh Abdulrashid Maccido.
Sa'idu wanda shi ne kuma Mallam Ubandoma Sokoto, ya ba masu sauya shekar tabbacin cewa zai tafi da kowa a harkokin jam’iyyar musamman a yanzu da aka fara yakin neman zabe. 
Kuma da izinin Allah PDP ce za ta lashe zabe mai zuwa. 
Ya bukace su da su kara himma wajen samo Karin magoya baya da tallata jam’iyyar da yan takararta a yankin.