2023: Tinubu Ya Sanya Rana Da Jiha A Arewa Don Ƙadamar Da Kamfen Ɗinsa

2023: Tinubu Ya Sanya Rana Da Jiha A Arewa Don Ƙadamar Da Kamfen Ɗinsa

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta tsayar da ranar 15 ga watan Nuwamban 2022, don kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasarta a Jos, babban birnin jihar Plateau. 
Hakan na cikin jadawalin da jam'iyyar ta fitar ne a ranar Laraba 3 ga watan Nuwamban 2023, The Punch ta rahoto. 
Hakan na zuwa ne makonni bayan hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta amince da fara yin kamfen na zaben 2023. 
Jam'iyyar ta APC, a lokuta da dama ta yi yunkuri fara yakin neman zaben amma ta dage saboda wasu dalilai. 
Amma, a jadawalin da kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasar ta fitar a ranar Laraba, jam'iyyar za ta fara yakin neman zaben shugaban kasarta a Jihar Plateau, yayin da za a fara tarukan sauraron ra'ayi tare da masu ruwa da tsaki a sassan kasar daga 16 zuwa 30 ga watan Nuwamba.
Jam'iyyar kuma ta shirya tuntubar masu ruwa da tsaki na kasashen waje daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Disamban 2022. A ranar 8 ga watan Fabrairun 2023, za a yi tattaki da bikin wakoki a birnin tarayya, Abuja, yayin da taron da za a yi na Legas shine na karshe a ranar 13 ga watan Fabrairu.