Abin da ya sa ban halarci taron kaddamar da jami’an tsaron Sakkwato ba---Sanata Lamido
Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a majalisar dattijan Nijeriya Sanata Ibrahim Lamido ya bayyana dalilinsa da bai samu halartar taron kaddamar da jami’an tsaro mallakar jihar Sakkwato a satin da ya gabata.
Sanata Lamido a hirarsa da manema labarai a jihar Sakkwato ya ce "duk dan adam yana da uzuri abin da ya hana min halarta taron ban da lafiya ne a ranar, kuma na kira jagoran siyasar jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Gwamnan jiha Dakta Ahmad Aliyu da Mataimakin Gwamna Injiniya Idris Gobir na sanar da su halin da nake ciki ba zan samu damar zuwa ba, harkar tsaro abu ne da ya shafi jihar Sakkwato bai kamata mutane su dauki abin da wata manufa ta daban ba," a cewar Lamido
Ya kake ganin tallafin kudi dubu 50 da ka baiwa dalibbai su dubu 11 zai yi tasiri ga karatunsu? ya ce "na farko mun yi abin da manufa kyakkyawa tsakani da Allah domin in taimaki yaran da ba su da hali su tafi su yi karatu ina ganin in yara suka samu ilmi da sana'a harkar ta'addanci ba za ta shiga ransu ba. Abin da muke yi don Allah ne hakan ya sa ba ruwanmu da yadawa, a majalisar dattawa in an bani naira 100 na mazabata ina da tabbacin kafin raba masu, sai na kara wata 100 sau 7 zuwa 10 sannan na raba, bana jiran abin da zan ba su kafin in yi masu hidima, muna yi ne tsakani da Allah domin mu taimaki al'ummarmu."
managarciya