Kotu ta Dawo da Lawal Dare Matsayin Halastaccen ‘Dan Takarar Gwamnan Zamfara a PDP

Kotu ta Dawo da Lawal Dare Matsayin Halastaccen ‘Dan Takarar Gwamnan Zamfara a PDP

Kotun daukaka kara ta shiyyar Sokoto ta tabbatar da Daura Lawal Dare matsayin ‘dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar Zamfara a zaben 2023, Channels TV ta rahoto.

Hakan na nuna ta soke hukuncin kotun tarayya da ke zama a Gusau wacce da farko ta fatattaki Lawal Dare.
A hukuncin babbar kotun tarayya, tace jam’iyyar PDP bata da ‘dan takarar gwamna a jihar a zaben 2023. 
A watan Satumba, kotun ta soke zaben fidda gwani na baya da aka zabi Lawal Dare wanda Ibrahim Shehu da wasu ‘yan takara biyu suka kai kara don kalubalantar ingancin zaben fidda gwanin. Kotun ta bukaci a sake zaben fidda gwani amma Lawal Dare ya sake samun nasara a watan Satumban. 
Daily Trust ta rahoto cewa, Dare ya samu kuri'u 431 inda yayi caraf da tikitin takarar gwamnan jihar Zamfara na jam'iyyar a zaben fidda gwanin da aka yi na ranar 25 ga watan Mayun 2022. 
Sauran 'yan takarkarin sun hada da Abubakar Nakwada, Wadatu Madawaki da Ibrahin Shehu Gusau wadanda da farko suka janye daga takarar saboda magudi. 
Sai dai Adamu Maina, wanda shi ne baturen zaben, yace ba a mince da janyewarsu ba tunda babu takardar da suka bayar matsayin sanarwa.