PDP  Ce Za Ta Karɓi Mulki  Hannun  APC A 2023-------Atiku Abubakar

Atiku ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a wurin taron zaɓen shugabannin PDP a matakin jiha a mazabar shi dake Jihar Adamawa. “Idan kuka duba zaku ga yadda zaɓen ke tafiya cikin adalci kuma ba ɓoye-ɓoye a lokuta da dama muna zama ne mu amincewa juna a kowane mataki.”

PDP  Ce Za Ta Karɓi Mulki  Hannun  APC A 2023-------Atiku Abubakar
Alamar Lema

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana yaƙininsa cewa 'yan Najeriya za su sake miƙa ragamar mulkin Najeriya ga jam’iyyar PDP a 2023.

Atiku ya roƙi 'yan siyasa su girmama dokokin zaɓen jam’iyya da kuma kundin tsarin mulkin ƙasa yayin gudanar da kowane irin zaɓe.

Tsohon mataimakin shugaban yana cewa matuƙar ana son ɗorewar demokaraɗiyya to sai an tabbatar da ingancin zaɓe. 'Yan Najeriya ba su da wani zaɓi da ya wuce jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Atiku ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a wurin taron zaɓen shugabannin PDP a matakin jiha a mazabar shi dake Jihar Adamawa.

“Idan kuka duba zaku ga yadda zaɓen ke tafiya cikin adalci kuma ba ɓoye-ɓoye a lokuta da dama muna zama ne mu amincewa juna a kowane mataki.”

Rahoto ya nuna cewa sama da wakilan PDP 2,614 daga ƙananan hukumomi 21 na jihar Adamawa ne suka kaɗa kuri’arsu a wurin zaɓen.

Zaɓen a jihar Adamawa ya gudana cikin lumana ba wata hatsaniya ko gardama kan gudanat da zaɓen.

Jihar PDP ce mulkinta kuma lamurran jam'iyar bai da wata tirjiya kumi lafiya lau.