PDP a Sakkwato ta fara shirin fitar da wanda zai gaji Tambuwal

PDP a Sakkwato ta fara shirin fitar da wanda zai gaji Tambuwal
PDP a Sakkwato ta fara shirin fitar da wanda zai gaji Tambuwal
Shugabannin jam'iyar PDP a yankin Sakkwato ta tsakiya ta gudanar da taron msu ruwa da tsaki na yanki domin tattauna lamurran jam'iya da bayar da katin jefa kuri'a.
A ranar Assabar din nan ne aka kira taron irinsa na farko cikin shekara shida na Mulkin Gwamna Tambuwal da zimmar duba sha'anin tattalin arzikin jiha da kasa baki daya kamar yadda aka ambata a rahoton da turakar mataimakin gwamna ta Facebook ta fitar.
Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan'iya(Walin Sokoto) ne ya jagorancin taron tattaunawar na masu ruwa da tsaki na PDP a dakin taron Otel din Giginya dake birnin Sakkwato.
Mataimakin Gwamnan ya yaba wa kokarin shugabannin PDP na yankin akan kiran taron na tattaunawa a karon farko tare da fatar za'a daure da yin sa a kowane watanni 3.
Manir Dan'iya ya bayyyana hobbasar gwamnatin kan harkar tsaro da tattalin arzikin jiha, kuma yayi kira ga wayarda kan mutane su karbi katin jefa kuri'a domin an bar jihar Sakkwato a baya.
Taron ya ba da damar shiga lamarin siyasa hadi da duba kalubalen da Jam'iyar PDP ke fuskata a jiha tare da nemo hanyoyin taimakawa 'yan jam'iya tare da baiwa Gwamnatin jiha Shawarwari na inganta sha'anin jindadin 'yan jiha.
Managarciya ta fahimci taron wanda aka shafe sa'a hudu ana yinsa an tattauna sha'anin na siyasa da lamurran jagoranci a jiha, abin da yake nunawa kenan hanya ce ake lalubowa ta fitar da wanda zai gaji Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a yankin Sakkwato ta tsakiya.
In aka yi la'akari da yanda jagororin PDP a yankin suka baiwa taron muhimmanci, amma aka kasa kiran manema labarai dake aiki a jihar Sakkwato abin ya fito karara magana ce ta 2023 ake nukunuku da ita.
Duba da yanda mataimakin gwamna tun sanda ya hau kujera mai matsayi na biyu a jiha ya kulle gidansa ga duk wani talaka da bai nema ba, ba wata kungiyar talakawa dake kai masa gaisuwar ban girma ba tare da izininsa ba, amma ka gan shi a yanzu ya jagoranci taron manyan 'yan siyasar yankinsa kasan magana ce ta wane ne zai gaji Tambuwal?.